Kasar da ake zubar da cikin ‘yan mata da aka yi wa fyade

A pregnant young woman with her hands over her belly

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Asibitocin gwamnati a Brazil kan zubar da cikii shida a rana ga 'yan mata tsakanin 10-14
    • Marubuci, Vinícius Lemos (@oviniciuslemos)
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Brasil

Melania Amorim na farkon kama aikinta a matsayin likitar mata da harkokin goyon ciki da haihuwa lokacin da ta fara fuskantar duba mai juna biyu da shekarun ƙuruciya.

Wata yarinya ce mai fama da larurar shanyewar ƙafafuwa da hannuwa, 'yar shekara 13 da aka yi wa fyaɗe a bayan gidansu, sa'ar da babarta take ciki tana aikace-aikace.

An kai ta wani asibiti da ke arewa maso yammacin Brazil don zubar da ciki - sai dai babu likitan da ke aiki a lokacin da ke son yi wa yarinyar wannan aiki.

"mahaifiyar yarinyar mai aikin wankau ce don haka ta bar 'yar tata a waje tana shan hantsi. Ta samu juna biyu bayan auka matan da aka yi," Dr Melania ta faɗa wa BBC.

"A asibitin, babu wanda ke son ko taɓa ta ma, saboda suna cewa ba sa goyon bayan zubar da ciki."

"Ina matashiya sosai, amma na yi mata aikin zubar da juna biyu. Ina da cikakken yaƙinin cewa ina kuɓutar da rayuwar yarinyar ne kuma hakan 'yancinta ne a matsayinta na wadda aka yi wa fyaɗe," likitar ta faɗa muryarta na shaƙewa.

Dr Melania ta yi aiki da yara ƙananan da aka yi wa ciki da 'yan mata a shekarun ƙuruciyarsu tsawon sama da shekara 30 kuma ta ƙware a fannin kula da 'yan matan da suka samu ciki bayan an yi musu fyaɗe.

Lamarin fyaɗe huɗu a rana guda

Al'ummar Brazil sun gigita da ka-ce-na-cen batun wata yarinya 'yar shekara goma da aka zubar wa ciki bayan kawunta ya yi ta yi mata fyaɗe. Lamarin ya faru ne a birnin Sao Mateus, da ke jihar kudancin ƙasar ta Espirito Santo,

Dr Melania Amorim in a zoom interview for BBC News Brasil

Asalin hoton, Reprodução

Bayanan hoto, Dr Melania Amorim ta yi aiki matasa masu juna biyu da kuma matan da aka yi wa fyaɗe tsawon sama da shekara 30

Lamarin ya shiga kanun jaridu ne bayan an ɗauki yarinyar inda aka tafi da ita zuwa wata jiha mai maƙwabtaka da mahaifarta don yi mata aiki - a can ne wani ɗan fafutuka mai tsananin ra'ayin riƙau ya fallasa bayanan ko wace ce ita.

Akwai kuma yunƙurin da aka sha yi na hana zubar mata da ciki a kotu har ma da zanga-zanga daga ƙungiyoyin addini - wasu masu fafutuka sun yi ƙoƙarin kutsa kai cikin asibitin da aka kwantar da yarinyar.

Dokar Brazil ta ba da damar zubar da juna biyu ne kawai idan an yi wa mace fyaɗe ko kuma rayuwar mai juna biyun tana cikin kasada.

Tuni wata kotu ta bai wa yarinyar 'yar shekara goma wadda kawunta ya keta mata haddi, damar zubar da cikin da ya yi mata.

Dr Melania ta ce sha'anin aikin likitanci irin wannan, abu ne da ya zama ruwan dare - kuma ita tana taƙama da ƙwarewar aikin da ta samu.

Cibiyoyin lafiyan Brazil na gwamnati kan samu a ƙalla buƙatun zubar da ciki shida a kullum ga 'yan matan da shekarunsu suka kama daga 10 -14.

Kididdigar matsalolin tozartawar jinsi ita ma tana da tsoratarwa: alƙaluman da wata ƙungiyar da ba ta gwamnati ba mai suna Brazilian Public Safety Forum ta tattara sun nuna cewa ƙananan yara mata huɗu 'yan ƙasa da shekara 13 ne ake yi wa fyaɗe duk cikin sa'a ɗaya a ƙasar.

Juna biyu mai hatsari ga 'yan mata

"Sun isa asibitin cikin firgici da ɗaurewar kai game da duk abubuwan da suka faru a kansu masu dugunzumarwa," likitar ta bayyana.

A pregnant lady moves around her humble accommodation in Brazil

Asalin hoton, Marcello Casal Jr./ABr

Bayanan hoto, "Juna biyu na da hatsari ga kowacce mace a kowanne mataki na shekaru," in ji Melania. "Sai dai hatsarin ya fi yawa idan 'yan mata ne."

Dr Melania ta ji taruwar abubuwa na "ɗaurewar kai da kakabi da ƙyama da hasala" sakamakon yunƙurin da aka sha yi don hana yarinyar 'yar shekara goma zubar da cikin.

Ana ɗaukar juna biyu a shekaru irin wannan a matsayin wani abu mai matuƙar hatsari.

Ƙwararru na nuni da cewa masu juna biyu da ƙuruciyarsu kamar 'yan shekara 15 ko ƙasa da haka, suna da yiwuwar mutuwa kusan sau huɗu a kan matan da suka girma.

Wani nazari da aka wallafa a Mujallar Cutukan Mata da Matsalolin Goyon ciki da Haihuwa ta Amurka ya yi tsokaci kan rayuwar matasa masu juna a Latin Amurka.

Inda ya gano cewa 'yan matan da shekarunsu ba su wuce 15 ba, na da yiwuwar samun matsanancin ƙarancin jini da kuma fuskantar wani gagarumin hatsarin zubar jini bayan haihuwa.

Hatsari ga jariri/jaririya

Akwai kuma ƙarin yiwuwar mutuwar fuju'a ga jariri sabon haihuwa.

Melania Amorim ta nunar cewa juna biyu tsakanin matasa 'yan shekara 10 zuwa 15 yana da gagarumin hatsarin haddasa jijjiga lokacin goyon ciki da naƙuda ko matsananciyar jijjiga - larurorin da kan haifar da bugawar zuciya fiye da kima har ma suna iya janyo dogon suma.

"Jariran da waɗannan 'yan mata za su haifa ba lallai ne su yi kumari ba. Girmansu taƙaitacce ne (saboda surar jikin mai juna biyu) kuma don haka da yawansu sai dai a haifo su bakwaini," in ji likitar.

Juna biyu ga 'yan mata masu shekara 13 ko ƙasa da haka ya ma fi hatsari saboda a lokacin ne jikinsu yake girma.

"Gangar jikinsu da halittun cikinsu ba su riga sun yi ƙwari ba. Ba su da, ga misali kwankwaso da ya ƙosa kuma wannan na iya hana ci gaban naƙuda," ta yi bayani.

"Haihuwa ta fi zubar da cikin hatsari ga irin waɗannan 'yan mata"

Dr Melania Amorim, wadda kuma farfesa ce a Jami'ar Tarayya ta Campina Grande, ta ce halartaccen zubar da ciki ya fi aminci ga irin waɗannan 'yan mata a kan su haihu.

"Haihuwa takan zo da kasada ga kowacce mace, kuma a kowanne matakin rayuwa. Ta ma fi hatsari ga 'yan mata," in ji ta.

A cewarta "abu mafi muni shi ne zubar da ciki maras aminci, wanda mace za ta yi shi a ɓoye".

Dr Melania ta kuma ce binciken da aka yi kan mata a ƙasashen da har yanzu ke bari a yi wa ƙananan yara auren wuri ya nuna cewa rahotannin 'yan matan da ake samu da ciwuka a cikin cikinsu tsakanin mafitsara da al'aura, suna da yawa.

"Sun samu juna biyu kuma sun haihu da taimako ko ba taimakon ƙwararru, ba kuma tare da samun aikin tiyata ba. Jariri zai yaga komai ya fito."

A pregnant girl leaning against a wall

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Juna biyu ga 'yan mata 'yan shekara 13 ko ƙasa da haka na da matuƙar hatsari saboda jikinsu bai gama girma ba

Melania Amorim tana kuma aiki da mutanen da suka fuskanci tozartarwar jinsi.

A matsayinta na likitar mata, ta yi wa matan da aka ci zarafinsu rakiya, waɗanda suka kama daga jaririya 'yar wata shida har zuwa tsohuwa mai shekara 92.

"Babu shekarun da suke kare mu daga fyaɗe. Mu mata ba mu tsira ba a kowanne matakin shekaru muke," ta ce.

"Lokacin da mace take matashiyarta, ko ba ta samu ciki ba. Amma dai al'amuran cin zarafi da yawa na farawa ne a wannan mataki kuma abin yana ci gaba har zuwa loacin da yarinya za ta fara sakin ƙwai daga mahaifa kuma, idan aka yi rashin sa'a, sai juna biyu ya shiga," Dr Melania ta ƙara da cewa.

"'Yan mata da yawa ba su da masaniyar cewa a dokance suna da 'yancin zubar da ciki"

Ba duk juna biyun da aka samu ba ne yake ƙarewa a zubarwa. Likitar ta ce wasu matasan da aka yi wa fyaɗe na isa asibiti ne jim kaɗan kafin su haihu.

"'yan mata da dama ba su san cewa suna da 'yancin zubar da ciki ba a ƙarƙashin doka."

Dr Melania ta tuna karon farko da ta duba batun mutuwar mai juna biyu lokacin tana 'yar shekara 17 sa'ar da take makarantar koyon aikin likitanci.

"Yarinya ce 'yar shekara 13 da ta rasu saboda zubar da ciki ta ƙarƙashin ƙasa. Kuma babban abin baƙin cikin ma shi ne tana da 'yancin zubarwar ta halartacciyar hanya," in ji ta.

A pro-abortion activist wears face paint with the word "legalize" written on

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dokar Brazil ta ba da damar zubar da juna biyu ne kawai idan fyaɗe aka yi wa mace ko kuma akwai hatsari ga rayuwarta

"Na samu masu juna biyu 'yan shekara 10 da jijjiga waɗanda sai da aka zura musu kororon taimaka wa numfashi bayan sun kusa mutuwa sakamakon matsananciyar ƙyarma."

"Babu wadda ta mutu a cikinsu. Amma dai kasadar rasa mutum idan an samu farfaɗiya, babba ce."

Nuns carry a "no to abortion" sign during a protest in Brazil

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zubar da ciki batu ne da ke matuƙar raba kan al'umma a ƙasar - waɗannan hadiman coci suna ɗaga wani rubutu da ke cewa "ba mu yarda da zubar da ciki ba" da harshen Portuguese