Cutar korona a Kaduna: An sanya ranar komawa aiki a jihar

Asalin hoton, @GovKaduna
Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta sanar da ranar komawa aiki ga ma'aikata a fadin jihar baki daya.
Cikin wata sanarwa da gwamnatin ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce ma'aikatan gwamnati a jihar da ke mataki na 14 za su koma bakin aikinsu daga ranar Litinin 20 ga watan Yuli da muke ciki.
Sanarwar ta ce wajibi ne ga dukkan ma'aikatan su zama masu bin dokar da mahukunta a bangaren kiwon lafiya suka shimfida.
Ta cikin sanarwar gwamnatin Kaduna ta ce masu mataki na 14 zuwa sama za su rika zuwa aiki ne a ranakun Litinin da Laraba da kuma Juma'a.
Amma daga masu mataki na bakwai har zuwa na 13 su za su koma bakin aiki ne daga ranar Talata, kuma za su rika zuwa aiki sau biyu ne kacal a sati a ranakun Talata da Alhamis daga karfe 9 na safe zuwa uku na rana.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Kaduna dai na cikin jihohin da annobar korona ta fara bulla a yankin arewacin Najeriya, kazalika tana cikin jihohin da suka fi daukar tsauraran matakan kariya a fadin kasar.
Ko a baya sai da gwamnan jihar Nasir El-Rufa'i ya rika kai ziyara babbar hanyar tarayya da ta ratso ta cikin jihar domin tabbatar da babu wanda zai shiga jihar yayin dokar kulle da aka sanya a fadin jihar.
Tun a watan Maris ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanya dokar takaita zirga-zirga tare da haramcin tafiye-tafiye tsakanin jihohi.
Sai dai daga baya sassauta wasu daga cikin wadannan dokoki yayin da wasu kuma ke ci gaba da aiki har ya zuwa yau.
Ya zuwa yanzu dai jihar Kaduna na da wadanda suka kamu da cutar korona da suka kai 1,099, yayin da 829 suka warke cikin har da gwamnan jihar suka warke kuma wasu 12 suka mutu.












