Majalisar Wakilai ta karrama Abba Kyari

Asalin hoton, @HouseNGR
Majalisar Wakilan Najeriya ta karrama DCP Abba Kyari, Shugaban Rundunar Sirri ta 'yan sandan Najeriya (IRT) ranar Alhamis.
Majalisar ta ce ta karrama ofisan ne mai muƙamin Mataimakin Kwamishinan 'Yan Sanda saboda jajircewarsa wurin daƙilewa tare da kama manyan masu aikata laifuka a Najeriya.
Kakakin Majalisar Femi Gbajabiamila ne ya miƙa masa kyautar a zaman majalisar na ranar Alhamis bisa gayyatar Honarabul Alhassan Ado Doguwa, Jagoran Majalisa.

Asalin hoton, @HouseNGR
Daga cikin nasarorin da Abba Kyari ya samu akwai kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane Chukwudi Onwuamadike (wanda aka fi sani da Evans) da Bala Hamisu (Wadume).
Sauran sun haɗa da waɗanda ake zargi da kisan tsohon babban hafsan sojin Najeriya Alex Badeh da kuma waɗanda ake zargi da yin garkuwa da sirikin dogarin Shugaba Buhari.







