Coronavirus: Halin da dan Atiku Abubakar yake ciki

Asalin hoton, Getty Images
Mohammed Atiku, dan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ce yana samun sauki tun bayan da aka killace shi sakamakon kamuwa da coronavirus.
A wani sakon bidiyo da mahaifinsa ya wallafa a Twitter, ya ce ko da yake lokacin da aka kai shi cibiyar killace masu dauke da cutar da ke Gwagwalada a Abuja, babban birnin kasar ya fada cikin fargaba da tashin hankali, amma babu abin da ya fi bata masa rai fiye da labaran karya da ake yadawa kan irin su da ke dauke da coronavirus.
A cewarsa, an fi watsa irin wadannan labarai kan irin sa da suka fito daga gidajen 'yan siyasa.
Ya ce yana sa ran kammala wa'adinsa na zaman wurin killace masu dauke da cutar, yana mai cewa "yau ina kwana na 11 zuwa 12, ina fatan barin wurin nan ba da dadewa ba, watakila idan sakamakon gwaje-gwajen da za a yi min suka kasance masu armashi."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Ya jinjina wa ma'aikatan lafiya da ke kula da masu cutar, amma ya bukaci jama'a su ci gaba da daukar matakan kare kansu daga kamuwa da cutar.
Waiwaye
Ranar 23 ga watan Maris, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya ce dansa ya kamu da coronavirus.
Atiku Abubakar, ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na twiiter.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce tuni aka kai dan nasa asibitin koyarwa da ke Gwagwalada a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya inda ake masa magani.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Atiku Abubakar ya bukaci al'umma da su saka dan na sa a addu'a.
Mutum 190 ne suka kamu da cutar a kasar zuwa yanzu, inda mutum 20 suka warke sannan biyu suka mutu.













