Ana shirin kwato wa almajirin da aka kona hakkinsa

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Kwanaki kadan bayan da BBC ta bayar da labarin wani yaro almajiri da aka azabtar ta hanyar jefa shi cikin murhun gasa biredi, har kafafunsa suka kone a garin Bajoga na jihar Gwambe, bisa zargin satar sunkin biredi, yanzu haka kungiyoyin kare hakkin dan adam da dama sun shiga maganar.

Har ma kungiyar kare hakki ta Civil Liberties Organisation reshen jihar ta Gwambe ta ziyarci yaron da wajen 'yan sanda da kuma gidan yarin da ake tsare da manajan gidan biredin da mataimakinsa wadanda ake zargin da azabtar da yaron.

Kuma kungiyar ta lashi takobin bin kadin batun, har sai an yi wa yaron adalci.

Shugaban reshen kungiyar ta Civil Liberties Organisation a jihar Gwamben, Muhammad Aliyu Wayas ya shaida wa BBC cewa sun yi tattaki har gidan malamin da kuma makarantar da wannan yaro yake don jin yadda lamarin ya faru.

Haka ma ya ce sun ziyarci asibitin da yaron yake kwance don ganin halin da yake ciki.

Sai dai duk da cewa yaron ya samu munanan raunuka, gwamnatin jihar Gwambe na ci gaba da kula da lafiyarsa.

Muhammad Aliyu ya ce sun garzaya gidan yari inda suka tabbatar da cewa ana tsare da manajan gidan biredin da kuma mataimakinsa, mutane biyu da ake zargi da wannan aika-aika.

Ya ce sabanin labarin kanzon kurege da ake ta yadawa musamman ta kafafen sada zumunta cewa an sake su, kungiyarsu ta tabbatar da cewa suna tsare hannun hukuma.

A kwanakin baya ne dai wani mai gidan biredi a garin Bajoga da ke jahar Gwambe ya jefa wani yaro almajiri dan shekara goma cikin magasar biredi, bayan ya zarge shi da satar masa biredi.

A wannan dalli ne ya sa ya kona masa kafafuwa.