Kisan rakuma a Australia ya fusata 'yan Somalia

Asalin hoton, Bidhaan Dahi
Wasu fusatattu a Somali na kira ga 'yan Australia da su daina yanke rakuma, inda suka ce a maimakon haka, su rika sakin dabbobin zuwa yankin Afirka domin a kula da su.
Gwanayen harbi na harbe rakuma a kudancin Australia daga sama tun ranar Laraba sakamakon damuwar da aka nuna cewa tsananin zafi da fari na tilasta wa dabbobin yi wa 'yan adam kutse domin neman ruwa.
Ana tunanin za a kashe dubban rakuman.
'Yan Somalia dai na sha'awar rakuma inda suke kiran su "geel". A kasar ana tantance arzikin mutum da matsayinsa ta yawan rakuman da yake da su ba wai yawan kudi ba.
Suna kuma ganin bayan Somalia ta kasance karkashin Turawan mulkin mallaka a karni na 19, sun kwace garken shanu tare da aike da su zuwa Australia wadda ita ma take karkashin mulkin Turawa.
Wasu kuma sun ce rakuma ne dabbobin da 'yan Burtaniya daga India da Afghanistan da gabas ta tsakiya suka fara aikewa Australia.
Sai dai Shugaban masu kiwon rakuma a Somalia, Mustafe Cali Deeq ya ce dabbobin suna da "matukar daraja" a wajen 'yan Somali.
Ya ce ya kamata Australia ta kyale rakuman sannan ta aika su asalin inda suka fito.
Yayin da wasu a shafin Twitter suka ce za su iya kiwon su a Mena, wani lakabin da suke kiran gabas ta tsakiya da Afirka.











