Ana tuhumar uwa da laifin kisan 'ya'yanta mata a mota

Kerri-Ann Conley

Asalin hoton, FACEBOOK

Bayanan hoto, Ana tuhumar Kerri-Ann da laifin kisan 'ya'yanta bayan samunsu a mace a mota a ranar Asabar

Ana tuhumar mata 'yar Australiya da laifin kisan 'ya'yanta mata biyu saboda tsananin zafi a mota.

'Yan sandan yankin Queensland ne suka samu gawar yaran 'yar shekara daya da biyu, a cikin mota a ranar Asabar. Kawo yanzu ba a san tsawon lokacin da suka dauka a cikin motar kafin su mutu ba.

Alamu sun nuna a jikin yara sun fuskanci tsananin zafi, kamar yadda wani jami'in dan sanda ya bayyana.

Tsananin zafin da ake yi a ranar ya kai maki 31 a ma'aunin salshiyos a kusa da garin Brisbane.

Mahaifiyarsu Kerri-Ann Conley mai shekara 27, ita ce ta farko da aka zarga da sanadin mutuwarsu bayan jihar Queensland ta kara fadada laifukan masu nasaba da kisa, ciki har da rashin bai wa rayuwar dan adam muhimmanci.

Ana kuma tuhumarta da laifin amfani da muggan kwayoyi da wasu abubuwa da ba su dace ba kamar yadda kamfanin kafar yada labarai ta ABC ta bayyana.

Shugabar 'yan sandan Queensland Annastacia Palaszczuk, ta bayyana lamarin da mai tayar da hankali tare da cewa sashen kula da kariyar yara zai duba lamarin.

''Abin ya taba min zuciya, na kadu matuka a lokacin da aka bayyan yadda aka samu gawar yaran,'' in ji ta.

Ta kara da cewa sashen kula da kariyar yara ya yi wa 'ya'yan Conley farin sani.

line

Matakan yadda za a kula da kariyar yara a mota

  • A ajiyewa yara 'yar tsana a cikin mota idan babu kowa a ciki, idan ka dora yaro kan kujera a mayar da 'yar tsanar kujerar gaba.
  • Tabbatar ka ajiye wayar salula ko takalminka tare da yaron a cikin mota
  • Ka tabbatar ka sanya bel a kujerar baya da ke bangaren mai zaman banza
  • Tabbatar ka duba kujerar gaba da baya kafin rufe motar
  • Shaida wa abokin zamanku ya kira don jin halin da yaran da aka sauke a wurin rainon yara suke ciki

Bayanai daga: Kids Safe Worldwide

line

An kira 'yan sandan Queensland a lokacin da aka ga motar, sun yi kokarin ba su taimakon gaggawa amma tuni rai ya yi halinsa.

Tuni aka fara ajiye furanni da katinan ta'aziyya a gidan iyayen yaran.

Jami'in tsaron da ke jagorantar binciken Mark White, ya ce ganau na ba su hadin kai don bincike lamarin.