Me ya fi dacewa bayan bahaya, tsarki ko sharewa?

Kwamin wanka mai hoton Sarauniya Victoria da tsohuwar taswirarr duniya a baya w

Asalin hoton, BBC/Getty Images

Bayanan hoto, A shekarun 1920 bandakin hoton nan abin ado ne

"A matsayinmu na Larabawa yana da matukar muhimmanci mu mallaki abubuwa akalla uku a lokacin da za mu yi kaura, wato Fasfo din tafiya, isassun kudade da kuma matsugunin tafi da gidanka,'' wannan kalaman wani mai wasan barkwanci Bassam Youssef kenan dan asalin kasar Masar, a lokacin da ya gabatar da wani wasa a Birtaniya a watan Yuni da ya wuce.

Ya ci gaba da zagaya dandamalin da ya ke gabatar da wasan akai, hannunsa rike da shayar wanka mai kama da macrofo.

''Ban fahimta ba, ku ne daya daga cikin kasashen da suka ci gaba a duniya, amma idan aka fara batun abu irin wannan ku ne a baya.''

Mutane da dama ka iya amincewa da kalaman Youssef.

"Alawar Cakulan"

Abin da yawancin kasashen yammacin duniya ke amfani da shi wajen goge bahaya maimakon takardar goge najasa ko amfani da hannu, shi ne wani karamin kwami idan mutum ya yi tsuguno a kai bututun da ke fitar da ruwan ya ke daidai al'aura ko dubura.

Mutane da dama sun amince ruwa ya fi tsarkake najasa fiye da takarda.

Mutanen da suka saba da amfani da ruwa don yin tsarki da ruwa kan tambaya wadanda ba sa yi me ya sa suke gogewa da takarda maimakon gwada amfani da ruwa?

Toilet douche

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tiyon wanke najasa ba sabon abu ba ne a kasshen turai

Ruwa ya fi zama abu mafi sauki da tsafta don wanke najasa idan aka kwatanta da sururun masara da turawan mulkin mallakar Amurka ke amfani da shi, ko wani faffadan abu da Girkawa ke goge najasa da shi, ya ma fi sauki fiye da takarda.

Ba kasashen yamma ne kadai ke amfani da nauyin tiyon tsarki ba, a Faransa ma suna amfani da shi.

Duk da cewa wannan nau'in ban-dakin bai zama sananne a Faransar ba, amma dai a kasashen Italiya da Argentina an dade ana amfani da shi.

Amma irin abin yin tsarki na tafi da gidanka da mai wasan barkwanci Youssef ya ke kira "bum gun," an fi samun nau'insa a kasar Finland.

Amma har yanzu a kasashen Amurka da Birtaniya da sauransu sun dogara da takardar goge najasa fiye da ruwa.

Kyanwa ta yi lakwam a kwamin tsarki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A Faransa ana amfani da wannan nau'in dan wanke hannu

Duk da haka ana amfani da ruwa don yin tsarki a kasashen musulmi, saboda koyarwar addinin musulunci ce hakan.

Mutum daya da ya fi karfafa amfani da takarda dan goge najasa shi ne mai kula da shirin gine-ginen gwamnatin kasar Australia wato Zul Othman, wanda ya yi zuzzurfan nazari kan tsaftace al'aura bayan kammala najasa.

Sai dai batun amfani da ruwa dan tsaftace jiki ba ga musulmai kadai ba.

Amfani da takarda

Wata mai binciken kimiyya 'yar kasar India mai suna Astha Garg, wadda ke aiki a birnin San Francisco sama da shekara biyu ta ce hankalinta kan tashi idan ba ta ga modar da ta ke dibar ruwa don yin tsarki ba.

A farkon zamanta a kasar sai da ta je wani kanti na 'yan Indiya sannan ta samu irin modar.

Wannan modar tana kama da abin da ake gasa biredi amma mai mariki, sannan da bututun da zai sanya ruwan zuba cikin tsanaki.

Takardar goge najasa ta kare

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tashin hankalin da mutane kan shiga idan takardar goge najasa ta kare da dadaddare

"Wasu Indiyawan na koyar da dabi'ar gogewa da takarda, amma yawancinmu gaskiya mun fi amfani da ruwa don ya fi tsafta,'' inji Asthma.

"A duk lokacin da kawaye na 'yan kasarmu suka zo daga Amurka na tabbatar zan ajiye musu muda ko jarkar ruwa da za su yi amfani da ita a kusa da matsuguni.''

Iyalan wani mawaki Kuo Kier sun samar da wata dabara don magance matsalar.

Shekaru uku da suka gabata suka yi kaura daga China zuwa Amurka, kamar kowanne bako a wata kasa sun yi kokarin morewa da al'adunsu na China tare da daukar na Amurkawa.

The longest 'toilet paper trails'. Annual per capita consumption in rolls.  .

Kuo ya kadu matuka a lokacin da ya lura da yawan takardar goge najasa da 'ya'yansa ke amfani da su sakamkon koyi da dabi'un Amurkawa. Da ya lissafa sai ya gano kowanne yaro da ya ya yi amfani da nadin takardar goge najasa guda 141 a shekara.

Ita ma Astha Garg ta ce abin na ba ta haushi. Baya ga kashe kudi takardar na yi wa muhalli illa indai ba a an dauki mataki ba, don wasu lokutan takan toshe sai an kira ma'aikata sun bude magudanar ruwa kafin ta wuce.

Dan haka Kuo ya samar wa iyalansa mafita, ta hanayr sayan kwami mai hade da Tiyo da ke yi wa mutum tsarki ba tare da ya sanya hannu ba.

Takardar goge najasa mai hoton dalar Amirka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Amirkawa sun fi kowa amfani da takardar goge najasa a duniya

Kamar yadda al'adun wasu kasashe suke, an yi amanna abu mai maiko ko ruwa-ruwa ya fi wanke najasa.

Salgar Bature

Salgar bature

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi amma bahaya ya fi wuce cikin sauki a Salga

Tsuguno don yin bahaya a salga ya fi komai sauki, da saurin wucewa.

Sai dai yawanci yara sun fi jin saukin tsuguno fiye da manya. Don haka ne a Amurka aka dade ba a amfani da irin shi, amma hakan ba ya na nufin babu shi kwata-kwata ba.

Idan mutum na zaune akan shaddar bature, ya kan dauki jarida ko littafi ya karanta, amma babu damar haka idan ana tsuguno akan Salga.