Rikici tsakanin Falasdinu da Isra'ila ya sake rincabewa

File photo showing Palestinian Islamic Jihad leader Baha Abu al-Ata at a rally in Gaza City (21 October 2016)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kungiyar PIJ ta sha alwashin daukar fansa kan mutuwar Abu al-Ata
Lokacin karatu: Minti 3

Wani harin sama da Isra'ila ta kai Zirin Gaza ya yi sanadin mutuwar wani babban kwamandan kungiyar mayaka masu fafutukar jihadi ta Falasdinawa PIJ.

Baha Abu al-Ata ya mutu tare da matarsa a lokacin da makami mai linzami ya fada gidansu, a cewar kungiyar. Rahotanni sun ce hudu daga cikin 'ya'yansu da kuma wani makwabcinsu sun ji rauni.

Firai ministan Isra'ila ya ce reshe ne ya so juyewa da mujiya don Abu al-Ata dama yana shirin kai hare-hare Isra'ilan.

A kalla rokoki 150 aka harba Isra'ila daga Gaza tun bayan kisan, wacce kungiyar ta PIJ ta sha alwashin daukar fansa.

Bayanan bidiyo, Ku kalli bidiyon yadda aka harba roka daga Zirin Gaza zuwa Isra'ila

'Yan Isra'ila 17 ne hare-haren rokokin suka ji wa rauni a kudanci, a cewar Cibiyar Lafiya Ta Barzilai Medical Center da ke birnin Ashkelon.

Ma'aikatan lafiya sun ce an kuma ji wa wata yarinya mai shekara takwas rauni kuma tana cikin tsananin hali bayan da ta fadi magashiyyan a yayin da iyayenta suka ruga wani waje don fakewa, lokacin da suka ji karar harba harin sama a Holon da ke kudancin Tel Aviv.

A kuma daidai lokacin da aka kai wa Abu al-Ata hari ne wasu mutum biyun suka mutu aka kuma ji wa mutum 10 rauni a wani harin sama da aka kai gidan wani dan kungiyar ta PIJ a birnin Damascus na Syria, a cewar kamfanin dillancin labaran Syria, Sana.

Aftermath of reported Israeli air strike on the home of a Palestinian Islamic Jihad leader in Damascus, Syria (12 November 2019)

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Kafofin yada labaran Syrian sun ce wani harin saman Isra'ila ya sake fadawa gidan wani dan kungiyar PIJ a Damascus

Kafar yada labaran Sana ta ambato cewa jagoran kungiyar PIJ Akram al-Ajouri, bai samu rauni ba amma dansa na daga cikin wadanda suka rasu. Amma sojin Isra'ila ba su ce uffan ba kan batun.

Hedikwatar kungiyar PIJ, wadda ke samun goyon bayan kasar Iran dai a birnin Damascus take, kuma daya ce daga cikin kugiyoyi masu karfi a zirin Gaza.

Shin me ya faru a Gaza?

Jiragen yakin Isra'ila su ne suka harba makamai masu linzami a wata unguwa da ke yammacin yankin Sheijaiya da ke Gaza da safiyar Talata, lamarin da ya haifar da tashin bama-bamai ana kuma iya hango yadda wuta ta tashi a wurin a nisan kilomita daga wurin.

Makami mai linzamin ya fada kan wani dogon gini inda ya lalata hawa na uku na gidan, ya kuma hallaka Abu al-Ata Ida mai dakinsa.

Yadda makami mai linzami ya lalata ginin gidan shugaban kungiyar jihadi ta Falasdinawa wato Baha Abu al-Ata

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Sojin Isra'ila sun ce sun kai hari gidan Baha Abu al-Ata

A sanarwar da kungiyar PIJ ta fitar, ta tabbatar da mutuwar jagoranta Abu al-Ata wanda shi ne babban kwamanda a arewacin Gaza.

Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya kira Abu al-Ata "mugun dan ta'adda," kuma shi ne yake kitsa hare-haren da 'yan ta'adda ke yi ga Isra'ila a Gaza.

Ya shaida wa taron manema labarai a birnin Tel Aviv cewa al-Ata shi ya kitsa tare da kaddamar da munanan hare-hare, ya harba makaman roka sama da 100 a unguwannin jama'a a zirin Gaza.

"Mun kuma ga yadda mutanen yankin suka shiga tashin hankali da kaduwa. Yana cikin shirin kai wani mummunan harin ne aka harba makamai masu linzamin a gidansa."

Shugaban ma'aikatan ma'aikatar tsaron Isra'ila laftanar janar Aviv Kochavi, ya ce Abu al-Ata ya raina irin shirin da Isara'ila ke da shi na kare kasarta a dan tsakanin nan, don haka ya saki jiki kamar babu abin da zai faru, duk da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kasar da kungiyar Hamas wadda ke iko da zirin Gaza da kishiyarta PIJ.

Map: Map of Israel and Gaza

Netanyahu ya yi gargadin cewa zaman lafiya zai yi kaura a Gaza matukar ba a daina tsokanar Isra'ila fada ba ta hanyar jefo makaman roka.

"Isra'ila ba ta da niyyar tabarbara lamura da karin tashin hankali, amma za ta yi duk mai yi don kare muradunta da al'umarta," in ji Netanyahu.

Presentational grey line