Jam'iyyar NDC na takaddama da masarautar Ashanti a Ghana

Sarkin Ashanti Otumfou Osei Tutu na biyu ya ce shi ne musabbabin wanzar da zaman lafiya bayan zaben shugaban kasar na 2016 wanda aka yi kan-kan-kan tsakanin shugaban kasa Nana Akufo Ado na jam'iyyar NP da tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC.
Sarkin ya yi wannann jawabi ne a taron Majalisar Dinkin Duniya a makonnin baya.
Ya ce wanda ya fadi zaben shugaban kasa yana da tababa kan sakamakon zaben abin da ya janyo zulumi da zaman dar-dar, abin da ya sa ya shiga tsakani don tabbatar da zaman lafiya.
Idan za a tuna zaben shugaban kasar Ghana na 2016 an yi kan-kan kan tsakanin shugaban kasa Nana Akufo Adoo da tsohon shugaban kasa John dramani mahama, inda wasu suke fara hasahen zuwa zabe zagaye na biyu, abin da ya dumama yanayin siayasar kasar a lokacin.
Sai dai da alama furucin da sarkin Ashantin ya yi a gaban majalisar bai yi wa babbar jam'iyyar adawa ta NDC dadi ba, inda ta mayar da martani a cikin wata sanarwar da ta fitar da rattaba hannun tsohon hafsan hafsohin fadar shugaban kasa, Julius Debra.
Ranar da shugaban kasa John Dramani Mahama ya amince da shan kayen zaben kasa, ya kira mataimakinsa Kwesi Bekoe Amissah- Arthur da shugaban jam'iyyar NDC Kofi Portuphy, da magatakardar jami'yyar Aseidu Nketia da wasu manyan jam'iyyar inda ya sanar musu da cewa zai kira shugaban kasa Nana Akufo Adoo ya taya shi murnar naasarar lashe zabe.
Duk da ya ce babbar jam'iyyar adawa ta NDC ba ta fito karara ta karyata sarkin Ashantin ba, sai dai a fakaice ta musanta maganarsa, lamarin da wasu magoya bayan sarkin suke ganin kamar bada wa sarkin nasu kura ne a ido.
Wannan lamarin dai janyo cece-ku-ce da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin wasu manyan jam'iyyar ta NDC da bangaren gwamnati inda ta fitar da sanarwa da rattaba hannun ministan watsa labarai Kojo Oppon Nkrumah, inda ya ce ta nuna bacin ranta dangane da yunkurin da wasu 'yan siyasa ke yi na raina sarkin Ashanti Otumofou Osei Tutu na biyu.
"Masauratun gargajiya suna da muhimmiyar gudunmawar da suke bayar wa a gwamnati, don haka bai kamata mutane ko 'yan siyasa su raina su ba," in ji Kojo.
A baya-bayan nan dai tsohon shugaban kasa John Mahama ya yi kokarin wanke kansa da jam'iyyarsa ta NDC inda ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, sanarwar da aka fitar daga ofishinsa an fitar ne don karin bayani kan abin da ya shafi zaben shugaban kasa na 2016 mai cike da cece-ku-ce











