Wata mata ta hadiye zoben baikonta cikin magagin barci

An engagement ring worn on a finger (file photo)

Asalin hoton, PA Media

Lokacin karatu: Minti 1

An yi wa wata mata a Amurka tiyata aka cire mata zoben baikonta da ta hadiye a cikin barci.

Jenna Evans mai shekara 29, ta ce ita da saurayinta Bobby suna cikin jirgin kasa sai aka tursasa mata ta hadiye zoben saboda yadda yake yi mata kariya daga "bata-garin samari."

Sai da ta farka a gidanta da ke California ta fahimci cewa ashe abin da ya farun mafarki ne amma kuma sai ba ta ga zoben daiman din nata ba.

Sai ta ce ta san ainihin abin da ya faru, sai ta tashi Bobby daga barci ta yi masa bayani, daga nan sai suka wuce asibiti.

Ms Evans ta ce "Da kyar na iya yi wa likitocin bayani saboda ina ta kuka-kuka dariya-dariya da karfi."

Kauce wa Facebook

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook

An dauki hoton cikinta sai aka gano zoben a ciki, sai likitocin suka ce ganganci ne a tsaya jiran sai ta yi bahayar zoben.

Daga baya aka yi wa Ms Evans aiki, amma ta ce sai da ta sanya hannu kan wani fom don nuna amincewa ko da rai zai yi halinsa.

Ta ce "Na yi kuka sosai saboda zan ji takaici idan na mutu. Na bata tsawon lokaci ina saka wannan tsinannen zoben baikon, kuma zan auri Bobby Howell."

An yi nasara a tiyatar, kuma Ms Evans ta ce ta farka bayan kammala tiyatar tana kuka mai tsanani.

"Na yi matukar farin ciki saboda ban sani ba ko zan iya ci gaba da son zoben nan," kamar yadda ta shaida wa kafar yada labarai ta ABC.