Hisbah ta kama almajirai 140 a Kano

Almajira a Kano

Asalin hoton, Getty Images

Hukumar Hisbah a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama almajirai kimanin 146 a ranar Litinin da daddare.

Hisbah ta ce ta yi kamen na sakamakon samun rahoton yadda kananan yara ke kai wa karfe 12 zuwa karfe 3 na dare suna gararamba, yayin da wasu kuma kan kwana a tasha da karkashin gada.

Hukumar ta ce hakan na kai wa ga an bata wa yaran rayuwa ko koyar da su aikata muggan laifuka.

Dr. Aliyu Musa Aliyu shi ne babban darakta a hukumar ta Hisbah, ya kuma ce tuni hukumar ta kira malaman wasu daga cikin almajiran an kuma ja musu kunne kan lallai su sa ido don hukumar ba za ta lamunci haka ba.

"Sun kuma ba mu tabbacin cewa hakan ba za ta sake faruwa ba, wasu mun mika ga su ga iyayensu, masu laifi daga cikin su kuma mun mika su hukumar Shari'a ta jiha," a cewar Dr Aliyu.

Sai dai al'ummar jihar na bayyana mabambantan ra'ayoyi kan kamun almajiran, inda mafi yawan mutane suka jinjinawa hukumar kan wannan hobbasa da ta yi.

Wasu kuwa na ganin gazawar gwamnati ce ta jawo hakan, ganin yadda ba ta bai wa malaman makarantun allon tallafin da za su kula da almajiran.

A shekarar 2014 ne aka kafa dokar kama masu bara a wani yunkuri na tsaftace titunan jihar Kano daga mabarata, amma sai dai dokar ta yi sanyi na tsawon shekaru biyar, sai a baya-bayan nan ta dawo da aiki.

An dauki tsawon lokaci ana tura yara almajirci a daukacin kasashen Hausawa da ke Afirka, musamman ma jahohin Maiduguri da Sokoto da kuma Kano.

Jahar Kano na daga cikin iahohi a Najeriya da gwamnatin kasar a mulkin Goodluck Jonathan ta fito da tsarin makarantun almajirai na zamani wato Tsangaya Model Primary School, a wasu daga jihohoin arewacin kasar, sannan aka bar su a karkashin kulawar gwamnatin jihohi.

A kwanakin baya ma shugaban Najeriya Muhamadu Buhari ya dora alhakin matsalar almajirai kan gwamnonin jihohi, alhakin da wasu daga cikin su suka dora kan gwamnatocin kananan hukumomi.