Gobarar dajin Amazon: Me ya sa hankalin masana da shugabannin duniya ya tashi?

An gano bakunan wuta dubu 72 a dajin Amazon

Asalin hoton, Reuters

A farkon mako ne sararin samaniyar Sao Paulo ya yi baki kirin, saboda wani gagarumin hadarin hayaki da ya turnuke.

Hayakin ya samo asali ne daga nisan kilomita 2,700, daga kungurmin dajin nan na Amazon mai matukar muhimmanci.

Dajin Amazon yana da girman murabba'in kilomita miliyan 5 da rabi, shi ne dajin da ya fi kowanne girma a duniya, kuma dajin yana a kasar Brazil ne da ke kudancin nahiyar Amurka.

Idan aka kwatanta, dajin ya fi girmar nahiyar Turai baki dayanta.

Ana wa dajin Amazon take da cewa shi ne 'mabubbugar iskar da dan'adam ke shaka' ta duniya.

Yana kunshe da nau'ukan tsirrai da halittu daban-daban kimanin miliyan 3.

Akwai mutane kauyawa miliyan daya da ke zama a kungurmin dajin.

Dajin yana taka muhimmiyar rawa wajen zuke sanadarin Carbon mai illa ga dan'adam.

Ana fitar da sanadarin Carbon ne daga hayakin motoci, da jirage, da kuma cibiyoyin samar da wutar lantarki.

Rashin isassun hanyoyin zuke sanadarin Carbon daga muhalli zai iya janyo illa ga duniya, daya daga cikin wadannan illoli shi ne dumamar yanayi da ake fama da shi.

Yadda hayaki ke tashi daga cikin dajin Amazon

Asalin hoton, Reuters

Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya ce 'A yayin da ake cikin rudani na sauyin yanayi, duniya ba za ta yadda ta kara lalata wannan muhimmiyar kafar samar da iska mai tsafta da halittu a duniya ba. Dole a kare dajin Amazon.'

Me kasashen duniya ke cewa kan gobarar Amazon?

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce ya yi magana da shugaban Brazil Jair Bolsonaro, inda ya ce Amurka a shirye take ta taimaka wa Brazil wajen kashe wutar dajin Amazon.

Faransa da Ireland sun yi barazanar cewa ba za su sake sabunta wata muhimmiyar yarjejeniyar kasuwanci a tsakanin su da kasashen kudancin nahiyar Amurka ba, face sai Brazil ta kara kaimi wajen kawo karshen gobarar dajin na Amazon.

A ranar Alhamis, shugaba Emmanuel Macron ya ce ya kamata a mayar da hankali wajen tattauna gobarar dajin Amazon a taron kashen manyan kasashen duniya 7.

Ministan kudi na Finland shi kuma ya yi kira ne ga kasashen Turai da su haramta shigo da nama daga kasar ta Brazil.

An gudanar da zanga-zanga a Barcelona kan gobarar Amazon

Asalin hoton, AFP

Wane ne ya tayar da gobarar?

Kasashen duniya suna dora laifin wannan gobara ne a kan shugaban Brazil Jair Bolsonaro.

Wani dan jarida na Brazil Silio Boccanera ya ce kasancewar yanzu lokacin rani ne a Brazil, dole za a yi tsammanin samun wutar daji.

Amma yanzu haka ana zargin cewa da gangan aka cinna wuta a wurare daban-daban na dajin.

Shugaba Bolsonaro ba ya sukan sare itatauwa a dajin na Amazon, kuma yana goyon bayan sare itatuwa domin gudanar da noma da kuma hakar ma'adanai.

Wane mataki ake dauka domin kashe gobarar?

Bayan shan matsi daga kasashe da kungiyoyi na duniya, a ranar Juma'a shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya umurci jami'an tsaro da su taimaka wajen kashe bakunan wutar gobara da suka balle a dajin nan na Amazon.

Wani umurni da shugaban na Brazil ya bayar, ya bayar da damar aikewa da sojojin suwa dazuzzukan domin ganin an shawo kan gobarar.

Wannan umurni da shugaban kasar ya bayar kamar yadda aka tsara za ta yi aiki ne tsawon wata guda, daga 24 ga watan August zuwa 24 ga watan Satumba.