Chandrayaan-2: Kumbon Indiya zai fara shawagi a duniyar wata

Asalin hoton, AFP
Shirin shawagi a sararin samaniya na biyu wanda kasar Indiya ta shirya ya fara zagaye duniyar wata, kusan wata daya bayan da aka harba shi, a cewar jami'an kasar.
Chandrayaan-2 ya fara shawagi a duniyar wata ne karfe 09:02 wato karfe 04:32 agogon GMT a ranar Talata.
Kumbon ya gama zagayawa a cikin minti 30, a cewar kungiyar Indiya da ke gudanar da bincike a sararin samaniya (ISRO).
Firai Ministan Indiya Narendra Modi ya yaba wa shirin tare da kuma bayyana shi "a matsayin babban ci gaba."
Jagoran ISRO, K Sivan ya ce hankalinsa ya ba shi cewa Chandrayaan-2 zai sauka a duniyar wata a ranar 7 ga watan Satumba kamar yadda aka kiyasta.
''Mun yi iya kokarinmu don tabbatar da cewa komai ya tafi daidai,'' kamar yadda ya bayyana wa 'yan jarida a yayin wata ganawa da manema labarai.
An harba Chandrayaan-2 daga tashar Sriharikota a ranar 22 ga watan Yuli, mako daya bayan da wata matsala ta hana a harba shi a lokacin da aka tsara harba shi tun farko.
Indiya na sa ran cewa shirin wanda aka kashe dala miliyan 145 shi ne zai zama na farko da ya sauka a kudancin duniyar wata.
A cikin watan da ya gabata ne dai kumbon ya fara tafiyar tsawon kilomita 384,000.











