Kun san abin da dokar aure a jihar Kano ta ƙunsa?

Asalin hoton, others
Gwamnatin jihar Kano ta yi bayani ƙarara kan tanade-tanaden dokar aure da take ta janyo muhawara a jihar da sauran shafukan sada zumunta.
Gwamnatin Kano ta bakin kwamishinan shari'a na jihar Barista Haruna Isa Dederi ta ce tabbas akwai dokar da ta yi bayani dalla-dalla kan yadda ya kamata mutane su riƙa gudanar da auratayyarsu a jihar.
"Doka ce da aka ƙirƙire ta tun 1988, kuma a sashe na biyar na dokar wannan bayani yake.
"Ba iya lefe kawai dokar ta haramta ba, amma a yanzu shi ne abin da ya fi ɗaukar hankalin al'umma," in ji kwamishinan.
A tattaunawarsa da BBC Haruna Dederi ya ce dokar ta yi bayani kan mene ne ya halasta da kuma mene ne aka haramta idan an tashi aure a jihar Kano.
"Lokaci zuwa lokaci akan sake bibiyar doka, domin sake mata fasali idan muƙatar hakan ta taso.
"Tsayin zamani da kuma buƙatuwar mutane kan sa a sauya doka, ko kuma a yi mata kwaskwarima. Kamar dai yadda ake yi wa kundin tsarin mulki na ƙasa," in ji Dederi.
Ya ce a iya saninsa babu wanda ya gabatar da bibiyar wannan doka domin sabunta ta, ko kuma sauya mata fasali.
A cewarsa matuƙar akwai doka, duk tsayin zamani idan ba a yi mata gyara ba tana nan a matsayin doka babu mai sauya hukuncinta.
An tambayi Dederi kan me yasa dokar ta ɗauki kusan shekara 36 amma da dama cikin al'umma ba su santa ba?
Ya ce ƙalubale ne masu yawa da suke janyo haka, inda ya fara da zayyana yawan dokokin da ake da su a tarayya da jihohi. Inda ya ba da shawarar kamata ya yi a haɗa kundin wuri guda domin taƙaita yawan dokokin.
Ƙalubale na biyu shi ne ɓangaren shari'a na buƙatar a riƙa wayar da kai kan irin waɗannan dokoki. Saboda ƙuduri baya zama doka sai ya bi matakai da dama, tun a lokacin matakan ya kamata a riƙa sanar da al'uma a kanta.
Kazalika idan majalisar dokoki ta jiha ta tabbatar da doka ya kamata a riƙa samar da sashe da zai riƙa shaidawa mutane dokar.
Masu aiwatar da dokar ma ya kamata su riƙa ilimantar da mutane game da dokokin da ake yi musu hukunci a kai, ba zai ranar da hukunci ya zo ba mutum ya ji ta a matsayin sabuwar doka a kansa.
Kwamishinna Haruna Isa Dederi ya amsa cewa akwai ƙarancin wayar da kan al'umma game da dokokin rayuwa da suka shafe su, wanda kuma haka aikin gwamnati ne.
Matashiya kan ce-ce-ku-cen dokar lefe

Asalin hoton, Abba Hikima
Wani lauya mai zaman kansa a Kano da ake kira da Abba Hikima ne ya fara waiwayar wannan doka, yana cewa ya yi hakan ne domin ya tunasar da samari kan lamarin da yake zamar musu "aliƙaƙai" yayin aure, wanda kuma ba dole ba ne.
Da yake lamarin ya shafi matasa kai tsaye, hakan ya sa lamarin ya zama babban mau'du'in da ya mamaye kafafen sada zumuntar yankin a cikin wannan mako.
Da yake tattaunawa da BBC Abba Hikima ya ce "abubuwa sama da 10 dokar ta haramta, to amma abin da ya sa ka fi jin maganar lefe saboda shi ne ya fi tsayawa samari a wuya,".
Wasu daga cikin abubuwan da dokar ta aure ta 1988 ta haramta sun hada da:
Ajo, Taron biki, Lefe,Gara da dai sauransu.
Abba Hikima ya turawa BBC wata takarda da ya ce ya samota ne daga cikin kundin dokar ta jihar Kano.

Asalin hoton, Abba Hikima
"Wannan doka tana da hukunci, hukuncin wanda ya karya ta shi ne zama gidan yari na wata byu.
"Duk laifin da yake da hukunci dokarsa ba ta stufa," in ji Abba Hikima.
Sharhi
Masana shari'a sun ce dokokin da ake tanada a kundi, ana sauya su ne idan sun ɗauki dogon zamani ko kuma idan aka samu sauyin hali a inda aka kafa dokar.
Kazalika dokoki su kan sha bamban daga jiha zuwa jiha, wanda hakan ke da alaƙa da al'adu da addinai da kabilu da dai sauransu.
A wasu jihohin doka ta haramta shan giya, a wasu kuma babu laifi halastaccen abu ne shan barasa. Wannan dalili ya sa ba za a iya samar da doka ga jihohi ba da za ta zamar musu gama-gari.











