Waiwaye: Komawar Shekarau PDP, matashin da ya kashe mahaifansa da tabarya

Ga wasu muhimman abubuwa da suka faru a wannan makon a Najeriya daga ranar Lahadi 28 ga watan Agusta zuwa Asabar 03 ga watan Satumba.

'Shekarau ya koma Jam'iyyar PDP'

.

Asalin hoton, SHEKARAU/ATIKU

Tsohon gwamnan Kano kuma ɗan majalisar dattawa Malam Ibrahim Shekarau ya koma jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya 'yan watanni bayan sauya sheka zuwa NNPP.

Wata majiya mai karfi da ke da kusanci da tsohon gwamnan ta shaida wa BBC Hausa cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar, ya gabatar wa Shekarau da tsare-tsarensa kuma sun amince da su.

Atiku Abubakar, ya bayyana komawar Shekarau a matsayin alamu na nasara ga jam’iyyarsu a zaben 2023 mai zuwa. 

Bikin karbar Shekarau ya sami halartar masu ruwa da tsaki a jam'iyyar ta PDP da suka hada da gwamnonin jihohin Sokoto da Taraba da Delta, sai tsohon mataimakin shugaban Najeriya Arc Namadi Sambo. 

Shekarau ya ɗauki matakin komawa PDP sakamakon abin da ya kira "rashin adalci" da Rabiu Kwankwaso ya yi musu, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jagoran jam'iyyar NNPP.

Tun farko dai Malam Shekarau ya nuna rashin jin dadinsa kan hanasu wasu muƙamai da kuma hana magoya-bayansa damar takara a NNPP.

Abin da ya sa muka raba wa 'yan sintiri bindiga 7,000 - Gwamnatin Zamfara

.

Asalin hoton, ZAMFARA STATE GOVERNMENT

Bayanan hoto, Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle

Gwamnatin jihar Zamfara a arewacin Najeriya ta tabbatar da ƙudirinta na samar da kimanin bindiga 7,000 domin bai wa wasu ƴan sintiri da za ta zaƙulo daga cikin al'umma don aiwatar da wani tsari da ta kira "Carrot and Stick Approach" don fatattakar ƴan bindigar da suka ƙi miƙa wuya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mai bai wa gwamnan Zamfara shawara kan harkokin yaɗa labarai, Zailani Baffa ne ya bayyana hakan ga BBC inda ya ce matakin da ake kai yanzu a wannan tsarin shi ne za a ci gaba da yaƙar waɗanda suka bijire wa sulhu, kamar yadda gwamnatin tarayya ta yanke hukuncin a zafafa yaƙarsu.

A cewarsa, matakin zai shafi kowane yanki da ƙauyukan da ke da matasa, da sarakunansu suka amince mutanen kirki ne, (Shugabannin Ƙananan hukumomi) za su ba da amincewarsu.

Tuni masana harkar tsaro a Najeriya suka fara bayyana matakin gwamnatin a matsayin abin yabawa saboda tsaron al'umma hakki ne na kowa.

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro a kasar Group Captain Sadiq Garba mai ritaya ya shaida wa BBC cewa babu laifi a dauki irin wannan matakin saboda sau da yawa ana samun koke-koke cewa jami'an tsaro ba su da isassun kayan aiki.

"Idan gwamnatocin jihohi ko gwamnoni suka kara musu don suma su ba da tasu gudummawa kuma zai kara karsashi kuma za su nuna cewa suna godiya da abin da sojoji da jami'an tsaron su ke yi."

A cewarsa, an kai matakin da ya kamata kowa ya ba da tasa gudummawar domin tabbatar da cikakken tsaro amma "duk wani taimako da za a yi ya zama taimako na kayan aiki, taimako na kudi hannu da hannu yana da nashi nakasun."

Jami'o'in jihohi a Najeriya sun fara yi wa ƙungiyar ASUU tutsu

Jami'o'i mallakar gwamnatocin jihohin Najeriya na ci gaba da komawa bakin aiki, duk da yajin aikin da kungiyar malaman jami'o'i ASUU ke yi a duk fadin kasar.

Al'amarin da ke nuni da yadda goyon bayan da yajin ke samu yake ta kara zaizayewa, yayin da kungiyar malaman ta yi tsayuwar daka kan matsayinta, cewa sai gwamnatin tarayya ta inganta manyan makarantun nata a sassan kasar.

Sai dai yayin da wasu ke kira ga bangarorin ASUU da na gwamnati da ke tattaunawa su rika taunawa suna hurawa don samar da mafita, wasu kuwa suna ganin daliban da yajin aikin ya shafa da iyayensu ne ba su dauki lamarin da muhimmanci ba.

Rahotanni dai sun ce, Jami'ar Jihar Gombe, ita ce jami'a ta baya-bayan nan da ta juya wa yajin aikin na kungiyar ASUU baya, bayan shigen wannan mataki da jami'o'in Jihohin Legas da Osun da Kwara da Kaduna da Ekiti suka dauka.

Kodayake kungiyar ta bayyana tababar kasancewar wasunsu a cikin mambobinta.

Farfesa Abdullahi Ashafa, Shugaban Jami'ar Jihar Kaduna na riko, ya bayyana dalilan bude tasu jami'ar, inda ya ce:"Abin ya tsawaita, babu dalili kuma cutuwa muke yi, ɗalibanmu suna zaune a gida, iyaye sun gaji da ganin ƴayansu a gida, mu ma mun gaji da zama a gida," in ji Farfesa Abdullahi.

Gwamnatin tarayyar Najeriya dai a makon da ya gabata, ta gayyaci shugabanni da iyayen jam'io'i, tare kuma da shugabannin gudanarwa na jami'o'in gwamnatin tarayya zuwa wani zama da za ta yi da su game da batun yajin aikin kungiyar malaman jami'o'in kasar.

Gidan Talabijin na Channels Tv ya ruwaito cewa sanarwar zaman wanda aka shirya yinsa ranar shida ga watan Satumbar 2022, na kunshe ne cikin wata wasika da hukumar gudanarwar jami'o'in kasar (N.U.C) ta aike wa shugabannin a kokarinta na shiga tsakani domin kawo karshen yajin aikin da malaman jami'o'in kasar ke yi.

Matashin da ya kashe iyayensa da tabarya a Jigawa

.

Asalin hoton, OTHERS

Rundunar ƴan sanda ta Najeriya ta ce ta cafke Munkaila Ahmadu mai shekara 37 da ya yi amfani da taɓarya wajen halaka iyayensa a jihar Jigawa a arewacin Najeriya.

Iyayen - Ahmad Muhammad ɗan shekara 70 wanda mai unguwar Zarada Sabuwa ne da mai ɗakinsa Hauwa'u Ahmadu mai shekara 60.

Wasu mutum biyu sun ji rauni a lamarin yayin da Munkaila ya yi amfani da taɓarya wajen lakaɗa musu duka kuma suna samun kulawa a babban asibitin Gumel da ke Jigawa.

Babu ƙarin bayani kan abin da ya sa ake zargin Munkaila da aikata haka amma mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta Jigawa DSP Lawan Shiisu Adam ya faɗa wa BBC cewa binciken farko ya nuna cewa Munkaila na cikin ƙoshin lafiya kuma ba ya ta'amali da ƙwaya.

"A ranar 1 ga watan Satumbar 2022 kimanin ƙarfe 11:30 mun samu rahoton cewa wani Munkaila Ahmadu mai shekara 37 ya kai wa wasu hari da taɓarya.

"Jami'anmu sun garzaya wajen tare da kai mutane huɗu zuwa babban asibitin Gumel inda likitoci suka tabbatar da mutuwar Ahmad Muhammad mai shekara 70 da mai ɗakinsa Hauwa'u Ahmadu mai shekara 60, iyayen Munkaila da ya tafka aika-aikar.

"Mutanen biyu da suka ji rauni Hakalima Ahmadu ta kasance abokiyar zaman Munkaila yayin da Kailu Bagudu kuma maƙoci ne da ya yi ƙoƙarin shiga tsakani a lokacin da aka kai harin.

Kakakin rundunar ya ƙara da cewa kwamishinan ƴan sanda ya ba da umarnin a mayar da Munkaila sashen binciken manyan laifuka domin a duba lamarin.

'Kudin fito ne dalilin tsadar motoci a Najeriya'

Kungiyar masu sayar da motoci a Najeriya ta koka kan wani tsari da hukumar kwastam ta yi, na yi wa wasu motocin da ake shigarwa kasar kudin-goro, dangane da kudin-fiton da hukumar ke karba a kan su. 

Kungiyar ta ce gwamnati ta kayyade kudin fiton ne a kan motocin da ba su wuce shekara goma da kerawa ba, kenan haka za a biya ko da mota ta fi haka tsufa.

Hukumar kwastan din tana karbar kudin fiton ne ta hanyar intanet da aka fi sani da e-valuation.Shugaban kungiyar masu sayar da motocin, Injiniya Prince Ajibola Adedoyin, ya shaida wa BBC cewa tsarin kudin fiton na cikin dalilan da suka sa motoci ke tsada, kuma sana'arsu na fuskantar barazana.

“Mun san cewa idan aka yi wannan to za a samu matsala sosai, saboda sun ce shekara 10 da kera mota watau motoci da aka yi daga daga 2012 zuwa sama, su ne kadai za a iya shigowa da su cikin kasar” in ji shi.

Ya ce da farko hukumar kwastam ta sa kudi a kan sabbin motoci amma kungiyar ta ki amincewa da haka, amma a tattaunawar da suka yi da jami'an kwastam daga bisani sun fada musu cewa za su yi la'akari da shekarar mota.

Sai dai kungiyar ta ce tun a wannan lokaci sun fada musu cewa za a samu matsala idan suka yi haka, a cewar Prince Ajibola.

'Manyan matsalolin da ke janyo wa Najeriya cikas'

.

Asalin hoton, photoshoot

Bayanan hoto, Ahmed Makarfi Ahmed Makarfi

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta bayyana manyan matsalolin da ke janyo wa Nijeriya cikas ta fuskar ci gaban ƙasa, da bunƙasar tattalin arziki da inganta tsaro.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Alhaji Ahmed Muhammad Makarfi ya ce idan aka sake bai wa jam’iyyarsa ta PDP dama a zaɓen 2023, za su kyautata al’amura.

Makarfi ya shaida wa BBC cewa da wuya rayuwar al'umma ta inganta idan kusan komai da take amfani da shi daga kasashen waje ake shigowa dasu 

“Ka ga dai duk wata kasa da za ta dogara a kan cewa kusan komai za ta shigo ne da shi tana cikin wahala, kuma kusan yadda muke kenan a  Najeriya.Ya kamata a ce gwamnati ta shimfida abubuwa a kasa da za su habaka tare da sarrafa abubuwa daban-daban da na ci, da na amfani da su, har ma a rinka fitar da wasu.”

“Haka ne zai sa darajar kudin kasar watau naira ta yi karfi, idan kuma ta yi karfi to ka ga wannan ba karamin al'amari ba ne, saboda zai kawo ci gaba a tattalin arziki kasa,” in ji shi.

Najeriya za ta karbo bashin N11trn

Gwamnatin ta Najeriya ta tabbatar da cewa za ta samu kan ta a wani yanayi na matsin tattalain arziki a badi, kasancewar sai ta yi rancen fiye da naira tiriliyon goma sha daya ta cike gibin kasafin kudin nan na badin.

Kazalika gwamnatin ta ce sai ta sayar da wasu kadarorinta yayin cike gibin kasafin kudin. Ibrahim Isa ya duba mana wannan batu, musamman ma yadda zai shafi tattalion arzikin Najeriyar.

Ministar kudin Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed ta shaida wa ƴan majalisar wakilan ƙasar cewa gwamnatin tarayya sai ta hada jibin-goshi wajen cike giɓin kasafin kuɗinta na badi…saboda ya żarta gibin da ta samu na bana. 

Gibin banan dai ya kai naira tiriliyon bakwai da doriya. Yayin da badin kamar yadda Ministar ta ce ya kai naira tiriliyon 12 da `yan kai.

Ministar ta bayyana haka ne lokacin da take kare tsarin kasafin kudin kasar a dunkule na shekara ta 2023 zuwa 2025, inda ta ce cike gibin kasafin kudin badi zai bukaci ciwo bashi ko rance da  sayar da wasu kadarorin gwamnati.

Ministar ta ce bashin da za a ci don cike gibin kasafin kudin badin ya wuce mizanin da ka'ida ta tanadar, cewa bai kamata a yi rancen da ya ɗará kashi 3 cikin dari na gundarin kasafin kudin ba.

Rasuwar Sarkin Funakaye mai shekara 45

.

Asalin hoton, MASARAUTAR FUNAKAYE

Sarkin Funakaye a Gombe, Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga na III ya rasu.

Watanni 15 da suka gabata aka naɗa sarkin bayan mutuwar babban yayansa Alhaji Abubakar Kwairanga a ranar 20 ga watan Mayun 2021.

Kafin rasuwarsa ma sarkin ya halarci wani taro a birnin Gombe tare da ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami. Babu dai wasu bayanai da aka fitar kan abin da ya yi ajalinsa.

Sai dai gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga masarautar da jiha da kuma kasa baki daya. A wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan yaɗa labaran gwamnatin Gombe, gwamna Inuwa Yahaya, ya ce Gombe ta yi rashin ɗa wanda ke da nuna jajircewa wajen ayyukan ci gaba da hadin-kai da haɓɓaka.

Gwamnan ya mika ta’azziyarsa ga iyalan sarki da masarautar Funakaye baki ɗaya. Alhaji Muazu Muhammad Kwairanga III ana yi masa kallon matashin sarki da ke da nuna ƙwazo da himma wajen ayyukan al’umma.

Ba zan sauka daga shugabancin PDP ba - Iyorchia Ayu

.

Asalin hoton, IYORCHIA AYU

Shugaban jam’iyyar PDP a Najeriya Iyorchia Ayu ya ce ko a jikinsa game da kiraye-kirayen da wasu suke yi cewa ya sauka daga kan mukaminsa.

Kazalika ya ce masu yin hakan yara ne da ba su fahimci manufofin kafa jam’iyyar ba. 

A hirarsa da BBC, tsohon dan Majalisar Dattawan Najeriyar ya ce a iya saninsa ‘yan kasar ne suka zabe shi bisa sharuddan da jam'iyyarsu ta shata.

Ya kara da cewa ko a lokacin da za su gudanar da zaben shugabannin PDP na kasa, an yanke cewar ba za a yi la'akari da bangaren da shugaban jam’iyyar ya fito ba wurin fid da dan takarar shugaban kasar. 

Sai dai Gwamnan jihar Ribas da ke kudu maso kudancin Najeriya ya yi barazanar sa hannu wajen faduwar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023.

Mista Wike na martani ne game da kalaman da shugaban jam'iyyar PDP ya yi yayin wata hira da BBC Hausa, inda ya ce ''masu kiyare-kirayen ya saukan yara ne da ba su fahimci manufofin kafa jam’iyyar ba''.

Amma a martanin da ya mayar game da kalaman na Ayu mista Wike ya siffanta shugaban PDP da cewa hadamamme ne wanda a kullum yake bin san ransa.

Gwamna Wike ya kara da cewa ''Na yi tunanin a matsayinka na shugaban jam'iyya wanda ke son jam'iyyarsa ta yi nasarar lashe zabuka, bai kamata ka yi abin da zai raba kawunan 'yan jam'iyya, haka kuma bai kamata ka nuna wa jam'iyya girman kai ba''.