Labarin wasu masoya ɗan India da 'yar Pakistan da suka ƙare a gidan yari

Hoton masoyan biyu

Asalin hoton, BANGALORE POLICE

Bayanan hoto, 'Yan sanda sun ce Mulayam da Iqra sun haɗu ne a intanet a 2020 lokacin korona

A watan Janairu, an kama wani Ba’indiye da ya taimaka wa wata ‘yar Pakistan da ta shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba ta kuma samu katin shaida na bogi.

Matar da ya taimaka matarsa ce.

Mulayam Singh Yadav, ɗan shekara 21 ɗan asalin India da Iqra Jeewani mai shekara 19 wadda ta fito daga Pakistan sun haɗu ne a intanet shekara uku baya, daga nan suka fara soyayya, kuma sun fara ne ta hanyar yin wsan Ludo. Amma sun san abu ne mai wuya su kasance tare.

Alaƙa tsakanin India da Pakistan ta jima a matsayin marar daɗi – makotan sun yi yaƙi tsakaninsu sau uku tun daga shekarar 1947, lokacin da India ke fafutukar neman ‘yanci ita kuwa Pakistan ta ƙirƙiri nata. Wannan ya sanya samun biza tsakanin ƙasashen biyu masu tarihi ɗaya yake da wuya.

A watan Satumbar da ya gabata ne, Mulayam da Iqra suka je Nepal, suka yi aure a can. Daga nan kuma suka tafi Bangalore babban birnin Karnataka inda suka ci gaba da rayuwa.

Rayuwar da suke yi mai daɗi ta koma ta wuya a watan Janairu- An tsare Iqra saboda ta shiga India ba ta hanyar da ta dace ba, shi kuwa aka kama shi saboda aikata laifin zamba cikin aminci da yi wa wani takardun ƙarya da kuma bai wa ɗan ƙasar waje wurin zama ba tare da cikakkun takardu ba.

An mayar da ita Pakistan a makon jiya, shi kuwa an ci gaba da tsare shi a gidan yari da ke Bangalore.

‘Yan uwan Yadav, wanda ke zaune a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin India, sun ɗimauta da kamun da aka yi masa.

“Muna fatan muga sun dawo gida,”. “Mun san abin da ke tsakanin India da Pakistan. Amma su masoya ne kawai,” in ji Jeetlal dan uwan Yadav.

Ko ‘yan sanda sun yi kamar sun yarda.

“Bayan shiga ba bisa ƙa’ida ba da takardun bogi, sai kuma labarin soyayyarsu,” in ji wani babban jami’in ‘yan sanda da ya nemi a boye sunansa.

Hoton masoyan biyu

Asalin hoton, JEET LAL YADAV

Bayanan hoto, Masoyan sun yi aure a bara, sai dai ba su ɗauki lokaci suna rayuwa ba tare.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Labarin soyayyar ya samo asali ne a 2020, lokacin kullen korona.

Yadav yana aiki a wani kamfanin kwamfyuta ne a matsayin jami’in tsaro da ke Bangalore ita kuwa Jeewani tana karatu ne a wata jami’a da ke Hyderabad a Pakisatan.

Sun fara wannan soyayyar mai nisa ne bayan sun haɗu a intanet. A lokacin Iqra na shan matsin lamba daga iyayenta na cewa sai ta fito da miji ta yi aure.

Ko da Yadav ya yi mata tayin aure, ta amince ta kuma tashi daga Pakistan ta tafi Dubai daga nan kuma ta shiga Nepal inda suka haɗu. A nan ne suka yi aure a wata majami’a.

Sai dai Jeewani ba ta da takardun da ake buƙata da za su ba ta damar zama a India, sai ‘yan sanda suka ce Yadav ya yi mata katin shaidar zaman India na ƙarya.

A cewar ‘yan sanda kullum Yadav mijinta na fita aiki amma ita babu inda take zuwa.

Sai dai ko da yaushe tana yawan kiran mahaifiyarta ta manhajar WhatsApp da ke India, wanda hakan ya ja hankalin ‘yan sanda suka rinƙa bibiyar sawunta.

“A yanzu babu wani laifi da ake tuhumarta da shi bayan shiga India ba bisa ƙa’ida ba,” in ji mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na Bangalore, kamar yadda ya shaida wa BBC.

BBC ba ta iya samun Iqra ba da iyayenta da ke Pakistan domin jin ta bakinsu.

Amma a farkon wannan makon ne mahaifinta ya tabbatar da cewa ta koma gida kamar yadda kamfanin dillancin labarai na PTI ya bayyana, sai dai sun ce ba sa son cewa komai kan wannan batu.

Mahaifiyar Yadav ta ce tana fatan gwamnatocin ƙasashen biyu za su yi ƙoƙarin sake haɗa ma’auratan biyu domin ci gaba da zamansu na aure.

“Ba mu damu ba kan cewa ita Musulma ce ko ‘yar Pakistan ce, kawai abin da muka sani surukarmu ce. Za mu kula da ita yadda ya kamata kamar yadda muke kula da shi.”