Chelsea ta ci karo da koma baya a Villa Park a Premier

Aston Villa

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Aston Villa ta yi nasara a kan Chelsea da cin 2-1 a wasan mako na 26 a Premier League da suka buga ranar Asabar a Villa Park.

Minti na tara da fara wasan Chelsea ta zura ƙwallon ta hannun Enzo Fernandez, haka suka je hutu Aston Villa ba ta samu damar farke wa ba.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne, Villa ta zura ƙwallo a raga ta hannun Marco Asensio, wasa ya koma 1-1.

Ana daf da za a tashi Villa ta kara na biyu a raga ta hannun Asensio, na biyu da ya zura a raga a karawar, hakan ya bai wa Villa damar haɗa maki uku a kan ƙungiyar Stamford Bridge.

Aston Villa ta yi nasara karo na uku a wasa 12 a gida da Chelsea a baya-bayan nan, ta yi canjaras biyu da rashin nasara bakwai.

Ita kuwa Chelsea ta kasa cin wasan waje karo na bakwai a dukkan karawa a bayan nan, har da rashin nasara karo na huɗu a jere.

Ranar 1 ga watan Disambar 2024, Chelsea ta doke Aston Villa 3-0 a wasan farko a kakar bana a Premier a Stamford Bridge.

Waɗan da suka ci mata ƙwallayen sun haɗa da Jackson da Fernandez da kuma Cole Palmer.

Da wannan sakamakon na ranar Asabar, Aston Villa ta koma mataki na bakwai a teburin Premier da maki 42, bayan cin wasa 11 da canjaras tara aka doke ta bakwai.

Ita kuwa Chelsea wadda ta yi nasara 12 a kakar bana da canjaras bakwai da rashin nasara bakwai, ta yi kasan teburi zuwa mataki na shida da maki 43.

Wasa biyar na Aston Villa a Premier:

Premier League ranar Talata 25 ga watan Fabrairu

  • Crystal Palace da Aston Villa

Premier League ranar Asabar 8 ga watan Maris

  • Brentford da Aston Villa

Premier League ranar Talata 1 ga watan Afirilu

  • Brighton da Aston Villa

Premier League ranar Asabar 5 ga watan Afirilu

  • Aston Villa da Nottm Forest

Premier League ranar Asabar 12 ga watan Afirilu

  • Southampton da Aston Villa

Wasa biyar na Chelsea a Premier League:

Premier League ranar Talata 25 ga watan Fabrairu

  • Chelsea da Southampton

Premier League ranar Lahadi 9 ga watan Maris

  • Chelsea da Leicester

Premier League ranar Lahadi 16 ga watan Maris

  • Arsenal da Chelsea

Premier League ranar Laraba 2 ga watan Afirilu

  • Chelsea da Tottenham

Premier League ranar Asabar 5 ga watan Afirilu

  • Brentford da Chelsea