Iran ta faɗaɗa haramcin yawo da karnuka a biranenta

An Iranian couple on a motorbike with their dog in front ride on a highway in Tehran in 2022

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An kuma haramta yawo da dabbobi a cikin motoci
    • Marubuci, Jessica Rawnsley
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Marubuci, Parham Ghobadi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Persian
  • Lokacin karatu: Minti 3

Mahukunta a Iran sun faɗaɗa haramcin da suka ƙaƙaba a biranen ƙasar kan yawo da karnuka a wuraren al'umma, inda suka kafa hujja da kare lafiyar al'umma.

Haramcin, wanda ya samo asali daga wani umarnin ƴansanda a shekara ta 2019, wanda ya haramta yawo da karnuka a babban ƙasar - Tehran, a yanzu an faɗaɗa shi zuwa ƙalla birane 18 cikin makonnin da suka gabata.

Haka nan an haramta yawo da karnuka a cikin mota.

Hukumomi na hana mutane mallakar karnuka tun bayan juyin juya halin Musulunci na Iran a 1979, inda ake kallon kare a matsayin dabba mai 'Kazanta' sannan kuma kiwonsa a matsayin wata ɗabi'a ta yammacin duniya.

Sai dai duk da haka nan, ana samun ƙaryuwar masu mallakar karnuka, musamman tsakanin matasa, kuma ana kallon lamarin a matsayin nuna turjiya ga hukumomi.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce a cikin kwanakin nan birane kamar Isfahan da Kerman sun fara aiwatar da haramci kan yawo da karnuka.

Wani jami'in gwamnati a birnin Ilam da ke yammacin ƙasar, inda ake da haramcin yawo da karnuka ya ce "za a ɗauki mataki na shari'a" kan mutanen da suka saɓa dokar, kamar yadda kafafaen yada labaru suka ambato shi yana cewa.

Sai dai tilasta amfani da dokara a shekarun baya ta gaza karaɗe ko ina, bayan da masu karnuka da dama ke yawo da dabbobin a Tehran da kuma wasu biranen ƙasar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Babu wata dokar gama-gari a ƙasar da ta haramta mallakar kare a faɗin ƙasar, sai dai yawanci shugabanni a yankuna kan kafa irin wannan doka yayin da ƴansanda ke koƙarin tabbatar an yi aiki da ita.

"Yawo da karnuka barazana ce ga lafiyar al'umma da zaman lafiyarsu da kuma walwalarsu," in ji Abbas Najafi, wani mai gabatar da ƙara a birnin Hamedan.

An sha kama masu karnuka ana ƙwace dabbobin daga hannunsu sanadiyyar yawo da su a bainar jama'a.

Yawancin masu karnuka sun koma yawo da su ne a cikin dare ko kuma a yankunan da babu yawan al'umma domin kauce wa shan kamu.

Shugabannin siyasa na gwamnatin Musulunci ta Iran na ɗaukar mallakar kare a matsayin abin da ya saba wa al'adun Musulunci.

Malaman Musulunci da dama na bayyana shafa karnuka da kuma taɓa yawunsu a matsayin "Najasa".

A baya jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya bayyana mallakar kare - ba domin kiwo ko farauta ko kuma tsaro ba - a matsayin "abin ƙyama.

A shekarar 2021, ƴan majalisa 27 sun yi allah-wadai da mallakar kare, inda suka bayyana shi a matsayin "abin da ke lalata walwalar al'umma" wanda zai iya "sauya tsarin rayuwar Musulunci na Iraniyawa."