Palmer da Saka suna cikin takarar gwarzon matasan Premier

Saka and Palmer

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

An fitar da ƴan wasa shida matasa da ke takarar ƙyautar gwarzon ɗan ƙwallon Premier League.

Ana kuma hasashen watakila ɗan wasan Chelsea, Cole Palmer zai lashe ƙyautar, bayan rawar da ya taka a kakar da ta wuce, wanda ya ci ƙwallo 22 da bayar da 11 aka zura a raga.

Saka wanda ya yi takara a bara, yana cikin masu sa ran lashe ƙyautar, bayan ƙwazon da ya yi a Premier League a kakar da ta wuce da kai wa wasan karshe a Euro 2024.

Saka, zakaran ƙyautar 2022/23 ya ci ƙwallo 16 ya bayar da tara aka zura a raga a Arsenal a bara, inda Gunners ta yi ta biyu a teburin gasar.

A bangaren Manchester United, tana da matasa biyu da ke takara da ya haɗa da Kobbie Mainoo, mai shekara 19 da kuma Alejandro Garnacho, mai shekara 20.

Sauran sun haɗa da Michael Olise, mai shekara 22, wanda ya koma Bayern Munich daga Crystal Palace da ɗan wasan Brighton, Joao Pedro, mai shekara 22, wanda ya ci ƙwallo 20 a dukkan fafatawa a bara.

Ƴan wasan matasa da ke takarar gwarzon Premier League

  • Cole Palmer
  • Bukayo Saka
  • Kobbie Mainoo
  • Alejandro Garnacho
  • Michael Olise
  • Joao Pedro

Za a sanar da gwarzon ƙyautar ranar Talata 20 ga watan Agusta a birrnin Manchester.