Wane irin burodi ya kamata mu riƙa ci?

Asalin hoton, Getty Images
Ko ka san cewa akwai nau'in burodi iri daban-daban - kama daga yanda ake yinsu da kuma abubuwan da ake yin burodin da su? Sannan ka san cewa irin burodin da kake ci ka iya yin tasiri ga lafiyarka?
Idan kai mai sha'awar cin burodi ne sosai to ya kamata ka san irin burodin da kake ci domin amfanin lafiyarka saboda akwai na'ukan burodi da dama musamman na manyan gidajen burodi na zamani.
Irin waɗannan burodi na zamani ko na kanti za ka tarar yawanci suna ɗauke da gishiri da sukari da maiƙo da sauran sinadarai na zamani.
Wasu daga cikin waɗannan abubuwa da ake yin burodin da su za ka ga masana kimiyya na gargaɗinmu a kan mu guje su saboda haɗarinsu ga lafiyarmu.
Idan har kuka yi la'akari da yadda ake yin ire-iren waɗannan burodi me zai hana ku jarraba yin burodin da kanku a gida?
Kodayake ba sai kun yi naku na kanku ba - akwai nau'ukan burodi daban-daban a manyan kantuna, to amma da wuya ku san wanda ya fi dacewa ko ya fi kyau ku ci.
To saboda waɗannan dalilai sai mu ce wane nau'in burodi ne ya fi dacewa da lafiyarmu?
Kuma me ya kamata mu duba idan za mu sayi burodi?
Yin burodi irin na masana'antar Chorleywood
A ƙarshe-ƙarshen shekarun 1950 masana kimiyya a masana'antar Chorleywood da ke Birtaniya sun ƙirƙiro wata hanya ta yin burodi mafi sauƙi da kuma sauri, fiye da a da.
Sun ƙara wasu sinadarai na maiƙo da yist da wasu abubuwa waɗanda amfani da su ya sa ake iya yin burodin cikin sauri da kuma sauƙi, sannan kuma burodin yana daɗewa bai lalace ba.
Wannan shi ne ya sa a yau kashi 80 cikin ɗari na burodin da muke ci ta wannan hanyar ake yinsu.

Asalin hoton, Melissa Hogenboom
Sourdough
Saɓanin wancan tsarin na Chorleywood da yawancin gidajen burodi suke amfani da shi a yau inda suke yin burodin cikin sauri da sauƙi, wanda kuma ba ya lalacewa da wuri, akwai wani nau'in kuma da ake yi wanda ba shi da sauri.
Wannan nau'in burodin yana da tsami-tsami ne saboda ba a sa mishi sinadarai masu yawa kamar sauran, sannan kuma akwai bambanci wajen sarrafa fulawar a yi shi.
Galibi abubuwan da ake haɗawa wajen yin wannan burodi , ruwa ne da garin fulawa da gishiri da kuma sinadarin tsami (sourdough).
Masu cin wannan nau'in burodi suna sonshi sosai - to amma abin ma da ya fi shi ne - amfaninsa ga lafiyarmu.
Bincike da dama ya nuna cewa mutane ba sa jin yunwa sosai idan sun ci irin wannan burodin saɓanin sauran nau'ukan burodi.

Asalin hoton, Getty Images
Hanyoyin yin burodi na zamani?
Yawanci ire-iren burodin da muke saye yau a manyan kantuna ana yinsu ne ta wannan hanya (Chorleywood) amma saboda a yau ana amfani da sinadarai da yawa shi ne ake kiransu na zamani (UPFs).
To wannan cakuɗe da sinadaran ya sa ake ganin suna iya haddasa cutar daji ga mutum.

Asalin hoton, Getty Images
Burodin alkama
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yawancin burodin da ake sayarwa yau a manyan kantuna ana yinsu ne da yawa a masana'anta kuma suna ɗauke da sinadarai da dama da ake amfani da su wajen yin burodi da yawa cikin sauri wanda kuma zai daɗe bai lalace ba.
Burodin da ake yi da yawa wato na kamfani yana ɗauke da wajen kashi 11 cikin ɗari na abinci gama-gari.
Kuma duk abincin da ke da sinadarai na zamani da yawa yana da alaƙa da matsalolin lafiya da dama.
To amma ya kamata a lura cewa nau'ukan abinci da dama suna iya kasancewa da irin waɗannan sinadarai, don haka masana ke gargaɗin da kada a yi wa irin waɗannan nau'ukan abinci kuɗin-goro a ce suna da illa ga lafiya.
Hanya ɗaya mafita ita ce idan za ka sayi burodi ka duba ka ga wanda ba ya ɗauke da sinadaran da ba ka sani ba. Kuma idan na kamfani za ka saya, zai fi dacewa ka sayi na alkamar da ba a cire mata ainahin sinadaranta ba maimakon ka sayi na alkamar da aka surfe aka cire mata sinadaranta na ainahi - wanda ake kira farin burodi kenan.

Asalin hoton, Getty Images
Burodin alkamar da ba a surfe ta ba sosai ya fi sa mutum ya jima bai ji yunwa ba saboda sinadaran yake ɗauke da su na alkamar.
Wannan saɓanin farin burodi wato na alkamara da aka surfe ta kusan gaba ɗaya aka cire yawancin sinadaranta - wannan nau'in burodi zai sa ka ji yunwa da wuri.
Idan har ba za ka iya barin farin burodi ka koma na alkamar da ba a surfe ba - wanda za ka ga yana da duhu ko ruwan ƙasa - to za ka iya sayen wasu nau'ukan na abinci da aka yi da irin wannan alkamar.
Akwai taliya ruwan ƙasa da shinkafa ruwan ƙasa da gugguru da dai abubuwa da dama.
Yin hakan kuwa ba don komai ba ne sai domin inganta lafiyarka - saboda sinadaran da ke cikin alkamar.
Sabon nau'in burodi
Kasancewar mutane da yawa sun fi sayen farin burodi wanda bai kai na alkamar da ba a surfe ba amfani a yanzu masana kimiyya sun ɓullo da wasu dabaru na sanya sinadarai na ainahi a cikin irin wannan burodi ta yanda zai fi amfani ga lafiyar jama'a.

Asalin hoton, Getty Images











