Chelsea ta ci wasanta na Conference League

Asalin hoton, EPA
Chelsea ta doke Copenhagen har gida a wasan zagayen 'yan 16 na gasar zakarun Turai ta Europa Conference League da ci 2-1.
Bayan shafe minti 45 na farko ba tare da kai wani mummunan hari ba, ƙungiyar ta Enzo Maresca ta ci ƙwallon farko minti ɗaya bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Kyaftin Reece James ne ya ci wa Chelsea ƙwallon farko bayan Marc Cucurella ya garo masa ita.
Chelsea ta ƙara ta biyu a minti na 65 ta hannun Enzo Fernandez, wanda ya shigo wasan daga baya.
Mai masaukin baƙi Copenhagen ta yi nasarar farke ƙwallo ɗaya lokacin da Gabriel Pereira murza ta da ka bayan Marcos Lopez ya bugo bugun tazara.
Za a buga wasa zagaye na biyu afilin wasa na Stamford Bridge ranar Alhamis, 13 ga watan Maris da ƙarfe 9:00 agogon Najeriya da Nijar.







