Rikicin da ya janyo masarautar Oyo ta yi shekara uku babu Sarki

Oba Lamidi Adeyemi

Asalin hoton, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi/Facebook

Lokacin karatu: Minti 5

Tun bayan da gwamnatin jihar Oyo ta sanar da naɗin Oba Akeem Abimbola Owoade a matsayin sabon Alaafin na Oyo ake ta cece-kuce dangane da naɗin nasa.

Wasu jiga-jigan ƙasar na iƙirarin cewa ba su amince da naɗin sabon Alaafin ɗin ba kuma gwamnatin jihar Oyo ba ta bin ka'idojin da aka gindaya na naɗa sabon sarki ba.

Shi kansa shugaban majalisar ƙolin masarautar (Oyomesi) Cif Yusuf Akinade Ayoola, wanda ke riƙe da matsayin Bashorun, yayin da yake zantawa da BBC News Yoruba, ya ce ya yi abin da Gwamna Seyi Makinde ke so kan batun sarautar ne saboda majalisar ba ta amince da naɗin Owoade ba.

Ya bayyana cewa sunnan da gwamnan ya sanar ya bambanta da wanda majalisar Oyomesi ta aika masa kuma majalisar ta riga ta maka gwamnatin Jihar a gaban kotu kan batun.

Wannan ba shi ne karon farko da ake samun cece-kuce kan batun sarautar Alaafin ɗin Oyo ba, saboda wani rikici makamancin wannan ya kaure kusan shekara 50 da suka gabata lokacin da za a naɗa tsohon Alaafin, Oba Lamidi Atanda Adeyemi.

Yadda sarki Adeyemi ya zama Alaafin a shekarar 1971

A ranar 25 ga watan Janairun shekara ta 1968 aka sanar da rasuwar Alaafin Bello Gbadegesin Ladigbolu II.

Bisa ga al'ada kuma bisa ga yadda aka gindaya a kundin dokokin jihar Oyo, gidaje biyu ne ke da gadon sarautar Allafin - gidan Agunloye, (wanda daga nan ne Alaafin Gbadegesin ya fito), da kuma gidan Alowolodu.

Da yake ana da yaƙinin cewa sarautar za ta koma gidan Alowolodu ne, sai ƴan gidan suka fara shirye-shiryen wanda zai gaji sarautar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An rawaito cewa a ranar 29 ga watan Junairu, jagororin gidan sarauatar Alowolodu suka yi taro inda suka tattara sunayen mutum huɗu da suke ganin sun cancanci sarautar daga gidan.

Suka aika da sunayen da suka zaɓa zuwa majalisar Oyomesi, amma majalisar ta yi fatali da jerin sunayen tana mai cewa ba a bi ka'idojin al'adunsu ba.

Bisa ga al'ada, sai Oyomesi ta aika buƙata a hukumance ga gidan sarauta, kafin ake aika mata da sunayen ƴan takara, kafin ta zauna ta zaɓi wanda ta ga cewa shi ne mafi cancanta.

Onigegewura ya rawaito cewar, a ranar ɗaya ga watan Junin 1968, sakataren majalisar dokokin jihar Oyo ya sanar da cewa sarautar zata koma gidan Alowolodu kuma aka buƙaci su aika da sunayen waɗanda za su yi takarar.

Wannan ya sanya aka kira taron shugabannin gidan inda wasu daga ciki suka buƙaci a aike da sunan mutum ɗaya, Alabi Oranlola Adeyemi, amma ba kowa ne ya manice da hakan ba inda daga baya aka yanke hukuncin aikewa da sunayen mutum 10, ciki har da yarima Lamidi Olayiwola Atanda Adeyemi.

Babaiyaji, Cif Sanda Moradesa, shugaban gidan Alowolodu, ya gabatar da waɗannan sunayen ga Basorun, shugaban Oyomesi.

Zaɓen Alaafin mai ilimin zamani

Oba Lamido Adeyemi

Asalin hoton, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi/Facebook

Tun a shekarun 1930, lokacin da wasu ke fafutukar ganin Najeriya ta samu ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka, kiraye-kirayen zaɓan sarakunan gargajiya masu ilimin zamani ke yaɗuwa a faɗin ƙasar, kuma Oyo ma ba a bar ta baya ba.

A taron da aka yi a gidan Bashorun, an tabbatar da cewa ba za a naɗa basaraken da bai yi karatu ba a matsayin Alaafin. Don haka aka fara tankade da rairaya, har sai da ya kai sunaye biyar ne kaɗai suka rage, cikinsu kuma guda biyu ne suka yi fice – Yarima Sanda Ladepo Adeyemi, da Yarima Lamidi Olayiwola Adeyemi.

Dukansu suna da ilimin zamani, Ladepo Adeyemi tsohon jami'in ƴansanda ne yayin da Lamidi Adeyemi ma'aikacin gwamnati ne a jihar Legas.

A ranar 1 ga watan Afrilu, Oyomesi sun haɗu don zaɓan daya daga cikin mutane biyar da suka rage. Baki daya suka zaɓi Lamidi Adeyemi a matsayin Alaafin, kuma labari ya bazu ko'ina cikin garin cewa Lamidi ne aka zaɓa.

Duk da cewa Oyomesi ya zaɓi Lamidi, amma har yanzu gwamnati ba ta fitar da wata sanarwa ta tabbatar da hukuncin na Oyomesi ba. An aika sunan Lamidi zuwa ofishin shugaban ma'aikata a Ibadan domin sanya hannu da kuma shelanta.

A Ibadan ne maganar ta sake zani, inda aka canza sunan basaraken da Oyomesi ta aika zuwa wani suna na daban. A maimakon Kwamishinan da ke kula da harkokin sarauta ya aika sunan Lamidi ga hukuma sai ya aika da sunan Ladepo Oranlola Adeyemi.

Ra'ayoyi sun bambanta a tsakanin masu naɗa sarki - Oyomesi kan wanda zai zama Alaafin a 1968

Cikin ƙanƙanin lokaci lamarin ya janyo rarrabuwar kawuna a tsakanin ƴan majalisar Oyomesi, inda Basorun da Yagba da Samu da Alapinni da kuma Akinniku suka bayyan cewa suna tare da Lamidi. Yayin da Ashipa da Laguna suka goyi bayan Ladepo.

Yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana kan wannan batun, wasu daga gidan sarautar ta Alowolodu suka fito suka fara iƙirarin cewa duka ƴan takarar biyu basu cancanci zama Alaafin ba inda suka miƙa sunan Yarima Tella Kakansi Adeyemi.

Ganin cewa an kasa warware batun sarautar Alaafin ɗin, gwamnan yankin Yammacin Najeriya na lokacin, Robert Adeyinka Adebayo, ya kafa wani kwamiti da zai binciki dalilan da suka haddasa cece-kuce kan batun.

A ranar 12 ga Yuni, 1968, kwamitin Obileye ya fara zama don sauraron korafe-korafe game da rikicin da ya dabaibaye batun sarautar ta Alaafin.

Bayan sauraron bahasi daga ɓangarori daban-daban, kwamitin ya bayyana Yarima Sanda Oladepo Adeyemi a matsayin wanda ya cancanta ya zama Alaafin ɗin Oyo.

Haka kuma aka bai wa Oyomesi mako biyu kacal ta kammala duk wasu shirye-shiryen da suka dace domin a naɗa sabon Alaafin, amma duk da haka Oyomesi ta dage kan cewa Lamidi Adeyemi za ta zaɓa a matsayin Alaafin.

Daga nan sai gwamnatin jihar Oyo ta sake daukar wani mataki ta nada jami'an da za su gudanar da aikin Oyomesi.

Oyomesi dai ta yi yunƙurin gurfanar da gwamnati gaban kotu kan matakin amma hakan ya ci tura domin kotun ta ce ba ta da hurumin sauraren ƙarar.

A lokacin da batun sarautar Alaafin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, Gwamna Adebayo ya ce za su jingine batun na wucin gadi domin tunkarar yaƙin basasar ake gwabzawa a Najeriya a wannan lokacin.

Don haka, aka kasance babu wanda ke riƙe da sarautar Alaafin har tsawon shekara uku.

A naɗa Lamidi a matsayin Alaafin

Oba Lamidi Adeyemi

Asalin hoton, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi/Facebook

An sake dawo da sarautar Alaafin a shekarar 1970 lokacin da aka naɗa Dokta Victor Omololu Olunloyo a matsayin kwamishinan sarauta da ƙananan hukumomi a Jihar Oyo.

Olunloyo, bayan ya yi nazari kan cece-kuce da ƙararrakin da suka taso a kan wannan sarautar, ya bayar da umarnin a sake gudanar da al'amuran naɗn sarauatar tun daga matakin farko.

A ranar 18 ga Nuwamba, 1970, mutanen Oyo sun yi tururuwa zuwa gidan Bashorun Akano don jin wanda Oyomesi ta ayyana a matsayin sabon Alaafin.

An kuma aika sunan Lamidi Olayiwola Adeyemi ga gwamnati don sanya hannu, kuma Gwamna Adebayo ne ya ayyana shi a ranar 18 ga Disamba, 1970.

A ranar 14 ga watan Janairu na shekarar 1971, Lamidi Olayiwola Atanda Adeyemi ya hau karagar mulki a matsayin Alaafin ɗin Oyo.