Atletico ta kammala sayen Alvarez daga Man City

Asalin hoton, Getty Images
Atletico Madrid ta kammala sayen ɗan wasan Manchester City, Julian Alvarez kan fam miliyan 81.5.
Kuɗin ya ƙunshi £ 64.4m da ƙarin tsarabe-tsarabe na £17.1m ga ɗan wasan tawagar Argentina.
Ya zama mafi tsada a tarihi da City ta sayar, wanda ya zarce fam miliyan 50 da Chelsea ta biya kuɗin Raheem Sterling a 2022.
Alvarez ya ce zai jira har sai an kawo karshen Argentina a gasar Olympics ta 2024 kafin ya yanke shawara kan makomarsa a City.
Daga baya mai masaukin baƙi Faransa ta fitar da kungiyar a fannin tamaula a ranar Juma’ar da ta gabata.
Pep Guardiola ya so Alvarez ya ci gaba da taka leda a Etihad, inda ɗan kasar Sifaniya ya sanar a cikin watan Agusta da cewar mai shekara 24 yana cikin waɗanda zai yi amfani da shi a bana.
Sai dai kamar yadda ya faru a baya City ta kasa hana ƴan wasa da ya haɗa da Ilkay Gundogan da Riyad Mahrez da Aymeric Laporte da suka yanke shawarar barin ƙungiyar.
Atletico, wadda ta amince da za ta ɗauki ɗan wasan Chelsea, Conor Gallagher, har yanzu ba ta cimma matsaya kan ƙunshin yarjejeniya da Alvarez ba.
Ɗan wasan Argentina, wanda ya koma City a 2022 kan fam miliyan 14.1 daga River Plate, ya ci kwallo 36 a wasa 106 da ya buga wa kungiyar da Guardiola ke horar wa.
Alvarez ya lashe kofi uku a kakarsa ta farko a Etihad, wanda ya lashe kofin duniya a Qatar a 2022 da kuma ɗaukar Copa America a 2024 a Amurka.











