Har yanzu Gomez na son barin Liverpool,Marseille ta sanar da kudin da za ta biya Nketiah

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan bayan Liverpool da Ingila Joe Gomez mai shekara 27 a shirye yake ya bar kungiyar a bazarar nan bayan yunkurin da ya yi na koma taka leda a Newcastle a watan daya gabata ya ci- tura. (Mail), external
Marseille ta na da anniyar biyan fam miliyan 17 ga dan wasa mai kai hari na Arsenal da Ingila Eddie Nketiah, mai shekara 25 ya yin da ake sa ran kungiyoyin biyu za su ci gaba da tattaunawa da juna a cikin kwanaki masu zuwa. (Telegraph), external
Crystal Palace a shirye ta ke ta amincewa dan wasan gabanta Jordan Ayew mai shekara 32 barin kungiyar a wannan bazara ya yin da kungiyar Leicester na sha’awar dan wasan. (Standard), external
Everton na son dan wasan gaba na kasar Paraguay Ramon Sosa, mai shekara 24, sai dai tana fuskantar gogaya daga Nottingham Forest a zawarcin da suke yi masa daga CA Talleres. (Teamtalk), external
Watakila Chelsea ta jingine kudin da ta nema a biyata idan tana son ta cimma matsaya da Atletico Madrid wajan cefanar da dan wasan tsakiyar Ingila Conor Gallagher. Bangarorin biyu sun kasa cimma matsaya kan fam miliyan 20 da Chelsea ke son a biyata. (Mail), external
Yunkurin da Leicester ke yi wajan ganin ta dauko dan wasan gefen Ingila Reiss Nelson mai shekara 24 daga Arsenal ya gamu da cikas saboda ba zata iya biyan kudinsa ba . (Leicester Mercury), external
Leeds ta yi wa dan wasan gefen Fenerbahce da Ingila Ryan Kent mai shekara 27 tayin fam miliyan biyu da rabi. Jose Mourinho ya kosa ya cefanar da tsohon dan wasan Rangers. (Haber Ekspres - in Turkish), external
Paris St-Germain ta amince ta sayi dan wasan tsakiya na Benfica da Portugal Joao Neves, dan shekara 19, a kan yuro miliyan 60 tare da biyan karin yuro miliyan 10 akan dan wasan tsakiyar Portugal Renato Sanches, mai shekara 26. (Fabrizio Romano), external
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Nottingham Forest na gab da sayan dan wasa gefe na Portugal Jota Silva mai shekara 24 daga Vitoria Guimaraes kan yuro miliyan 7 a yarjejenuiyar da ta kunshi karin kudi na yuro miliyan biyar . (Sky Sports), external
Wolves da Fulham sun bi sahun sauran kungiyoyin kwallon kafa da ke rige- rigen daukar dan wasa mai tsaron baya Faransa Isaak Toure dan shekara 21 daga Lorient (Football Insider), external
Fulham ta amince ta rattaba hannu kan yarjejeniyar sayan dan wasan tsakiyar baya na Sfaniya Jorge Cuenca mai shekara 24 daga Villarreal. (Fabrizio Romano), external
Sai dai kawo yanzu Fulham ba ta sauya shawara a kan ko za ta sake bada aron dan wasanta mai kai hari a wannan bazarar ba. Dan wasan Ingila Jay Stansfield mai shekara 21 ya zira kwallaye 13 da aka bada shi aro ga Birmingham City a kakar wasannin bara . (Standard), external
Coventry City na zawarcin dan wasan gaban Ghana wanda kuma ke taka leda a West Brom Bradon Thomas Asane mai shekara 25 wanda Hull City ta yi masa tayin fam miliyan biyu da rabi. (Telegraph), external











