Dogon Mai Takwasara ya buge Muslim Autan ɗan Digiri

Damben gargajiya
Lokacin karatu: Minti 1

Dogon Dogo Mai Takwasara ya doke Muslim Autan ɗan Digiri a damben gasa ranar Lahadi a gidan wasa na Idris Bambarewa.

Damben na gasa ne na naira 100,000 tsakanin ɗan wasan Guramada da na Kudu da suka kece raini a Ƴan tifa a karamar hukumar Karo a jihar Nasarawa Najeriya.

Tun farko sai da Labaran ɗan Gwamba ya wake Dogon Dogo, sannan Muslim ya sha kida, daga baya suka shiga cikin fili.

Turmin farko ya yi ƙyau, saboda sun bugi juna sun kuma burge ƴan kallo, waɗanda suka yi ta yin tafi.

Bayan kammala turmin farko suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu ne Dogon Dogo Mai Takwasara Guramaɗa ya yi nasara a kan Muslin daga Kudu.

Ɗaya wasan gasar shima na naira 100,000 tashi aka yi canjaras tsakanin Aljanin Bahagon Nasarawa daga Jamus da Bahagon Yahaya Guramaɗa.

Turmi uku suka yi amma ba a samu gwani ba, kowanne turmi minti uku, sannan hutun minti ɗaya.

Haka kuma wasa na uku da aka tsara yi tsakanin Garkuwan Cindo Guramaɗa da Zazu na ɗan Ali daga Kudu, ba yi ba, saboda Zazu bai samu zuwa filin ba.

Idris Umar Bambarewa ya yi kokarin sa dambe da Garkuwan Cindo, bayan da ya jawo matasa uku, amma tsohon Sarkin ya ce sun yi yara ba zai yi dambe da su ba.

Wasannin da ak yi kashe-kashe:

  • Dan Dabar Sabon Gundumi ya buge Shagon Ɗan Aliyu
  • Shagon Yalo ya yi nasara a kanAutan Zango
  • Shagon Shagon Buhari ya doke Shagon Mabilu

Damben da aka tashi canjaras:

  • Nepa Autan ɗan Bunza da Pastor na Mai Takwasara
  • Shagon KD da Shagon Mabila
  • Ɗan Dabar Autan ɗan Bunza da Mabilu