Cutuka uku da suka tayar da hankalin hukumomin lafiya a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Aƙalla jihohi biyu tare da babban birnin Najeriya, Abuja ne suka fuskanci ɓarkewar wasu cutuka a makon da ya gabata da wanda ake ciki, al'amarin da ya tayar da hankalin al'umma da hukumomi.
Jihar Adamawa ta samu ɓarkewar wata baƙuwar cuta mai zagwanye naman jikin mutum da ta yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai.
Ita ma jihar Kaduna ta samu ɓarkewar cutar da hukumomi suka ce mashaƙo ce wadda ta kashe yara biyu sannan ta tilasta rufe makarantun jihar.
Ita kuwa Abuja babban birnin Najeriya ta samu wasu marasa lafiya guda biyu da wani nau'in zazzaɓi da ke sa mutane zubar da jini amma hukumomi sun ce ba a sami marasa lafiyar da Lassa ko kuma Ebola ba.
Cuta mai zagwanye naman jikin ɗan'adam
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN ya rawaito cewa cutar da ta yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai a jihar Adamawa tana farawa daga ƙuraje.
Daga nan kuma sai su fashe tare da zagwanyewa inda wani lokacin ma suke siɗe fatar har su tarar da ƙashi a gaɓar da cutar ta shafa.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta bayyana cutar ƙuraje ta Buruli Ulcer da ɗaya daga cikin cutukan da ba a fiya mayar da kai a kansu ba a duniya.
WHO ta kuma cutar na ɓarkewa a karkara musamman da ke kusa da ruwa da ke fama da rashin asibitoci.
Jami'i a shirin ƙasa na daƙile cutar tarin fuka da kuturta a Najeriya, Dr Adesigbin Olufemi ya sanar da cewa an samu masu ɗauke da cutar su 67, inda za a yi wa mutum 8 tiyata.
Olufemi wanda ya bayyana hakan a ranar Lahadi ya ce duk da cewa ba a gano dalilin faruwar cutar ba amma an fi zaton cewa cutar ƙuraje ce ta Buruli Ulcer wadda ake ci gaba da binciken gano bayanai a kanta.
Zazzaɓi da aman jini a Abuja

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja ya fuskanci wata baƙuwar cuta a ƙarshen makon da ya gabata, al'amarin da ya jefa al'ummar birnin cikin razani da fargaba.
Bayanai dai sun nuna cewa an samu wasu mutum biyu da zazzaɓi mai tsanani tare da aman jini ta baki da hanci da ta dubura a wani asibit da ke birnin.
Bayanai sun nuna cewa ɗaya daga cikin mutanen ya yi bulaguro zuwa ƙasar Rwanda domin yawan buɗe idanu, inda kuma tun a Rwandar ya fara fuskantar alamun cutar.
Ba tare da ɓata lokaci ba sai asibitin ya sanar da hukumar da ke daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya, NCDC wadda kuma ta umarci jami'anta su y gwaje-gwaje domin gano ko cutar na da alaƙa da zazzaɓin cutar Ebola da Marburg da Dengue da kuma na Lassa.
Sai dai kuma hukumar ta ce gwaje-gwajen da jami'an nata suka gudanar ba su sami cutukan da suke zargi ba.
Hukumar Lafiya ta Duniya dai ta bayyana cutar zazzaɓi mai sa aman jini da cutar da ke faruwa sakamakon ƙwayoyin cutar virus da ke illa ga jijiyoyin jinin ɗan'adam sannan kuma ka iya haddasa aman jini.
Tuni hukumomi ciki har da hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta Kano ta gargaɗi al'ummar jihar da su kula da shigi da ficin al'umma kasancewar jihar na da tarihin shigi da fici kasancewarta cibiyar kasuwanci.
Mashaƙo a Kaduna

Asalin hoton, Getty Images
Sakamakon ɓarkewar cutar ta mashaƙo da ta yi sanadiyyar mutuwar yara guda biyu ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke Kaduna, hukumomi sun rufe makarantu a yankin na tsawon mako guda.
Kwamishiniyar lafiya a jihar Dr. Umma Kulthum Ahmed ta ce an rufe makarantun ne saboda kaucewa ƙaruwar yaɗuwar cutar a tsakanin dalibai, ganin cewar yara ƙanan ne suka fi kamuwa da cutar.
Fiye da mutum 40 aka killace da suka kamu da cutar sai dai daga bisani an sallami wasu da dama daga cikinsu.











