Me ya sa mutanen Isra'ila ke zanga-zanga?

Katuwar tutar Isra'ila tsakanin masu zanga-zanga a Isra'ila a birnin tel aviv.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Dubban Isra'ilawa ne suka hau tituna domin yi wa Netanyahu zanga-zanga.
    • Marubuci, Jasmin Dyer
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 5

An gudanar da yajin aiki na farko a Isra'ila tun bayan harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba, bayan dubban mutane sun yi zanga-zanga a birane da dama a faɗin ƙasar.

An ci gaba da zanga-zanga ne a fadin ƙasar bayan gano gawarwakin mutum shida da aka yi garkuwa da su a kudanci Gaza.

Taron mutane zagaye a filin zanga-zanga.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga na ƙona abubuwa tare da toshe manyan hanyoyin birnin Tel Aviv.

Me ya sa sai yanzu ?

Masu zanga-zangar na zargin Firaiminista Benjamin Netanyahu da hana cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin da ake yi a Gaza domin sakin Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su domin cimma muradansa na siyasa.

Tun da dadewa iyalan waɗanda ake tsare da ƴan'uwansu suka yi watsi da salon yadda Netanyahu yake tafiyar da lamarin, amma fushinsu ya ƙaru ne bayan gano gawar mutum shida da sojin Isra'ila suka yi a wani rami a yankin kudancin Gaza.

An ce gawarwakin sun haɗa da na Carmel Gat da Eden Yerushalmi da Hersh Goldberg-Polin da Alexander Lobanov tare da Sarusi da kuma Master Sgt Ori Danino.

An gama tsara za a saki uku daga cikinsu in da an cimma ɓangaren farko na yarjejeniyar tsagaita wuta da aka tattauna a watan Yuli.

Masu zanga-zangar sun riƙa wake suna cewa "kai ne shugaba, kai za a zarga".

Watanni 11 ke nan da Hamas ta kai harin watan Oktoba, amma har yanzu ana riƙe da mutane a gaza, yayin da ake hasashen 33 a cikinsu sun mutu.

5

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wakilan ƙasashen Amurka da Masar da Qatar suna ta aikin shiga tsakani domin ganin yarjejeniyar tsagaita wutar ta yi aiki an saki sauran mutum 97 da har yanzu ake rike da su, duk da cewa ana tsammanin 33 daga cikinsu sun mutu - a kuma yi musayarsu da Falasdinawan da aka riƙe a matsayin fursunoni.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Mene ne masu zanga-zangar ke so?

Tattaunawa domin tabbatar da an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da za ta kai ga sakin mutum 97 da ake riƙe da su, ita ce babbar buƙatar masu zanga-zangar.

Sharone Lifschitz,mahaifiya ce ga ɗaya daga cikin waɗanda har yanzu ake riƙe da su a Gaza, Oded, ta shaida wa BBC kisan mutane shidan nan "shi ne abin da muke tsoro a ko da yaushe" wanda hakan na da nasaba da jan ƙafar da aka yi wajen tattaunawa da Hamas.

Ta ce saƙonsu a bayyane yake kuma za su ci gaba da nanata hakan har sai an cimma yarjejeniyar da "za ta dawo da mutanenmu gida, a kuma dakatar da wannan yakin na rashin tunani."

Ƙungiyar iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su ta ce duka mutum shidan da aka kashe, an kashe su ne ba da jimawa ba, bayan jure watanni 11 da suka yi ana gana musu azaba, da cin zarafi da yunwa daga Hamas.

"Jinkirin yarjejeniyar ne ya kai ga kashe su da sauran waɗanda aka yi garkuwa da su,"

Wane ne ya shirya zanga-zangar?

Masu zanga-zangar sun fantsama kan tituna ne bayan samun labarin ganin gawar mutum shida cikin waɗanda aka yi amannar suna raye, da aka boye a Gaza.

Daga nan sai aka ci gaba da kiran fitowa zanga-zangar da kuma yajin aikin gama-gari.

Histadurt, ita ce babbar ƙungiyar ƴan kasuwa ta Isra'ila, kuma ita ce take shirya yajin aikin tun watan Oktoban 2023.

Iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su sun yi kira ga ɗaukacin Isra'ilawa su fito zanga-zangar ta gama-gari domin tsayar da ƙasar da sauran ayyukan yau da kullum.

Jagoran ƴan adawar Isra'ila, Yair Lapid wanda shi ma tsohon firaiminista ne ya fito ya nuna goyon bayansa ga masu zanga-zangar, inda ya yi kira ga mutanen ƙasar su fito zanga-zangar.

L

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Yajin aikin ya shafi kasuwanci da makarantu da harkokin sufuri a faɗin Isra'ila, yayin da aka rufe tituna da yawa an kuma dakatar da tashin jirage da dama.

Me gwamnatin Isra'ila ke yi?

Benjamin Netanyahu ya yi watsi da duk wani labarin da ke cewa shi ne ke hana yarjejeniyar tsagaita wutar aiki, inda shi kuma yake ɗora laifin kan Hamas.

Yace Isra'ila ba za ta huta ba har sai ta kama waɗanda suka yi wannan kisan.

Jami'in Hamas, Izzat al-Rishq ya yi zargin ƙin amincewar Isra'ila ga yarjejeniyar ce ta kai ga mutuwar mutanen da aka kama, sai dai bai faɗi yadda aka yi mutanen suka mutu ba.

Bayan kawo tsaiko da aka yi a kan tituna da bankuna da makarantu da filayen tashin jirage, kotun ma'aikta ta Isra'ila ta yanke hukunci cewa dole a dakatar da yajin aikin da misalin ƙarfe 14:00 na ƙasar, amma masu zanga-zangar suka ci gaba har zuwa yammaci.

Tun da fari an tsara za a yi yajin aikin ne na kwana biyu a jere.

Minsitan kuɗin Isra'ila, Bezelel Smotrich wanda aka sani da ra'ayin riƙau, ya kira yajin aikin wanda ya saɓa wa ƙa'ida kuma ya yi maraba da hukuncin kotun.

Ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant, wanda tun tuni ya shawarci Netanyahu ya tattauna kan tsagaita wutar, ya wallafa a shafinsa na X cewa suna nan kan bakarsu ta neman tattaunawa domin tsagaita wutar.

"Lokacin ya ƙure wa waɗanda aka yi garkuwa da su da aka kashe. Waɗanda aka ɗauka suke a hannun Hamas dole su dawo gida," kamar yadda ya wallafa.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

Mene ne mutanen Isra'ila ke cewa kan zanga-zangar?

Dubban Isra'ilawa ne suka fito domin nuna goyon baya ga iyalan waɗanda suke hannu, duk da cewa wasu garuruwan sun ce ba za su shiga zanga-zangar ba.

Tamara daga Tel Aviv ta ce ita ba ta amince da yajin aikin ba: "Muna son a dawo da waɗanda aka kama gida, amma ba ma son a dakatar mana da harkokinmu; muna buƙatar mu rayu."

Niva wadda ke zaune a Tel Aviv - ta ce ta yi mamakin ganin shaguna da dama a buɗe ana tsaka da yajin aikin.

Ta shaida wa BBC "Ƙasar nan tana cikin wani irin ruɗani, Netanyahu ba ya sauraron mutane.

"Ya kamata a sauya abubuwa da dama a ƙasar nan. Me ya sa za mu riƙa rayuwa cikin tsoro ne?"

Wane tasiri zanga-zangar za ta yi wa gwamnatin Netanyahu?

Wannan zanga-zangar ita ce mafi girma da aka yi a Isra'ila, tun bayan ta 7 ga watan Oktoba lokacin da Hamas ta kai hari - Ana gudanar da ita ne da nufin matsa wa gwamnati ta mayar da hankali wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Yayin da ake ta nuna fusata kan firaiministan, da wuya idan zanga-zangar za ta yi wani tasirin a zo a gani ga salon gwamnatinsa.

Alistair Burt, tsohon ɗan majalisar Consevative ne kuma ya yi aiki a ofishin ministan harkokin wajen Burtaniya, ya shaida wa BBC cewa "Saboda Netanyahu ya faɗa tarkon waɗanda ba sa son cimma yarjejeniya da Hamas cikin ƴan majalisarsa, shi ma yanzu ya ja dagar ganin ya cimma abubuwan da ya yi alƙawari, duk da cewa ba abubuwa ba ne masu yiwuwa."