Raphinha na kan hanyar kafa tarihi a Barcelona

Asalin hoton, EPA
Lokacin da Rapinha ya isa sansanin Barcelona kafin fara kakar wasa ta bana, bai taɓa tunanin zai shiga kakar wasansa mafi ƙayatarwa ba.
Ɗanwasan na Brazil ya fara kakar ne bayan kaka biyu marasa kyawu da ya buga, bayan komawa Barca kan fam miliyan 55 daga ƙungiyar Leeds United a 2022.
Tun daga lokacin ne kuma ɗan shekara 28 ɗin ya jagoranci Barca wajen neman cin kofi uku. Yanzu ita ce a saman teburin La Liga da tazarar maki huɗu, sannan ta kai wasan ƙarshe na gasar Copa del Rey.
A ranar Laraba kuma ƙafarta ɗaya ta kai zagayen semi fayinal a gasar zakarun Turai ta Champions League bayan doke Dortmund 4-0 a wasan farko na kwata fayinal.
"Wasa 23 kenan ba tare da an doke Barcelona ba. Za su karɓi ƙwallon su hana abokan karawa taɓawa, kuma ba sassautawa idan aka ba su sarari," a cewar mai sharhin wasa Karen Carney a tashar TNT Sports.
Wannan kaka ce mafi kyawu a wajen Rapinha, inda tuni ya ci ƙwallo 28 kuma ya bayar aka ci 20 a dukkan gasanni.
Ƙwallon da ya ci Dortmund ta sa ya kamo Lionel Messi a yawan ci da kuma bayarwa a ci ƙwallo a kaka ɗaya ta gasar Champions League.
Bayan ya ci a minti na 25 da kuma wadda ya bai wa Lewandowski da Yamal suka ci sun sa ya bayar da gudummawar cin ƙwallo 19 cikin wasa 11 a kakar bana, irin adadin da Messi ya taɓa kaiwa a wasa 11 a kakar wasa ta 2011-12.
"Kana iya kwatanta shi da abin da Messi ya yi yayin da ya rage saura wasa huɗu kacal," kamar yadda Stephen Warnock ya shaida wa BBC Match of the Day.
Yanzu gudummawar cin ƙwallo uku kawai Rapinha ke buƙata domin ya karya tarihin da Cristiano Ronaldo ya kafa a kakar wasa ta 2013-14 a Real Madrid lokacin da ya ba da gudummar cin 21 a wasa 11.
Damarmaki 34 da ya ƙirƙira ga abokan wasansa a Champions League ta sa ya kamo adadi mafi yawa da aka yi a bana.
Wannan bajinta da yake ci gaba da yi ta sa ya shiga sawun masu neman kyautar gwarzon ɗanƙwallon duniya ta Ballon d'Or ta 2025.
"Ina jin daɗin taka leda da 'yanwasa masu ƙwarewa sosai," in ji shi bayan wasansu da Dortmund a daren Alhamis. "Muna ci gaba da ruwan ƙwallaye kuma ina fatan hakan zai ɗore."











