Barca ta yi wasa 24 a jere ba tare da an doke ta ba bayan cin Leganes

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta ɗauki fansa a kan Leganes da cin 1-0 a wasan mako na 31 a La Liga da suka kara ranar Asabar a Estadio de Butarque.
Sai da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne Barcelona ta ci ƙwallo, bayan da Jorge Sáenz ya ci gida.
Leganes ta yi nasara a gidan Barcelona 1-0 a La Liga wasan farko a bana ranar Lahadi 15 ga watan Disambar 2025.
Da wannan sakamakon, Barcelona ta yi wasa 24 a jere a dukkan karawa ba tare da an doke ta ba.
Rabon da Barcelona ta yi rashin nasara a wasa tun cikin Disamba, bayan da Atletico Madrid ta yi nasara 2-1.
Cikin wasa 24 a jere da Barcelona ta yi a dukkan fafatawa ba tare da rashin nasara ba ta yi canjaras huɗu daga ciki.
Ta tashi 1-1 ga Getafe a La Liga cikin watan Janairu da yin 2-2 da Atalanta a Champions League a cikin Janairu da 4-4 da Atletico Madrid a Copa del Rey cikin Fabrairu da tashi 1-1 da Real Betis a La Liga cikin watan Afirilu.
Ranar Talata 15 ga watan Afirilu, Barcelona za ta kara da Borussia Dortmund a Champions League a Jamus.
Ranar Laraba Barcelona ta caskara Dortmund da cin 4-0 a wasan farko a kwata fainal a gasar zakarun Turai a Sifaniya.
Daga nan kuma Barcelona za ta kece raini da Celta Vigo a La Liga ranar Asabar 19 ga watan Afirilu.
Barcelona tana matakin farko a teburin La Liga da maki 70 da tazarar maki bakwai tsakani da Real Madrid da tazarar maki 10 tsakani da Atletico Madrid ta uku.
Ranar Lahadi Real Madrid za ta kara da Alaves a wasan mako na 31, kuma saura wasa bakwai-bakwai a kare kakar bana.
Sai a ranar Litinin Atletico za ta kece raini da Valladolid, wadda take ta karshen teburin La Liga na kakar nan.











