Hezbollah ta kai harin roka a yankin Golan da Isra'ila ta mamaye

Golan Heights

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Hezbollah ta ƙaddamar da gomman harin roka a yankin Golan da aka mamaye, bayan wani jirgin yaƙin Isra’ila ya kai hari cikin Lebanon.

Ana kuma zaman fargabar ɓarkewar yaƙi tsakanin ɓangarorin.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce harin da ta kai cikin dare ya faɗa kan wurin ajiyar makaman Hezbollah da ke tsibirin Bekaa.

Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce harin ya kashe mutum ɗaya ya kuma raunata wasu 30.

Domin mayar da martani ne kuma, Hezbollah, wadda Iran ke goyon baya ta ce ta kai wa wata cibiyar sojin Isra’ila hari a yankin Golan. Hukumomin Isra’ilan sun ce harin ya faɗa kan wasu gidaje biyu, kuma mutum ɗaya ne kacal ya samu rauni.

Haka nan kuma, ƙungiyar Fatah ta Falasɗinu ta zargi Isra’ila da kisan wani babban jami’in ta a Lebanon, a wani yunkuri da ta ce na neman tunzura rikici ne a baki ɗayan yankin.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kashe Khalil al-Makdah a wani hari a birnin Sidon da ke kudanci saboda hannun da yake da shi a safarar makamai zuwa gaɓar Yamma da kogin Jordan.

Da yake jawabi yayin wata ziyara da ya kai rundunar sojin saman sa da ke kudancin Isra’ila, Firaiminista Benjamin Netanyahu ya ce a shirye ƙasarsa take ta kare kanta daga duk wani hari.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ce: "Na zo nan ne domin domin in gane wa idona shirin da muka yi domin kare kanmu daga duk wata barazana, ta nesa da ta kusa.

A shirye muke domin fuskantar kowanne irin yanayi, ko dai na kare kanmu ko kuma na kai hare-hare. Rundunar sojin saman mu itace hannun ƙarfen da muka dogara a kai domin murƙushe duk wata barazanar abokan gaba.

Idan buƙata ta taso za mu sake tabbatar wa duniya hakan, kuma wannan karon sai abin ya fi na baya muni.’’

Rahotanni sun ce wannan ne hari na farko a kan ƴan ƙungiyar Fatah tun bayan fara yaƙin Gaza, kuma ya ƙara lalata alaƙa tsakanin Isra’ila da Hezbollah.

Zaman fargaba ya ƙaru a makonnin nan bayan Isra’ila ta kashe wani babban kwamandan Hezbollah a Beirut, wanda ta ce yana da hannu a harin roka da ya kashe kananan yara 12.

Kawo yanzu mutane 530 aka ruwaito cewa an kashe a Lebanon, daga cikin su akwai fararen hula 130, yayin da aka kashe mutum 49 a Isra’ila, ciki harda fararen hula 26. Aƙalla mutum dubu 200 kuma aka tilastawa barin muhallin su daga dukka ɓangarorin.