Mai neman ƙaguwa da masu buɗe-baki a hotunan Afirka

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A wata ziyarar aiki ranar Talata a Ghana, mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris da mijinta sanye da kayan gargajiya na Kente da Sabarina Kwesi Atta II ya ba su.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A dai wannan ranar a jikin bango an manna hoton ɗan wasan Najeriya Victor Osimhen a wani titi da ke ƙasar Italiya tare da abokin ƙwallonsa.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani masunci na neman ƙaguwa a cikin tekun Dakar babban birnin Senegal ranar Asabar.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Fitaccen ɗan fim ɗin nan ɗan asalin Birtaniya da Zimbabwe Rege-Jean tare da magoya baya a lokacin nuna wani fim cikin Los Angeles ranar Asabar.
.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Sai kuma fitacciyar tauraruwar Afirka ta Kudu Thuso Mbedu da ta shiga ɗakin gabatar da shirin a birnin kwana guda kafin taron.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Lahadi Sarki Philippe na Belgium yana sa hannu kan wani zane a birnin Cape Town na Afirka ta Kudu.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, 'Yan sanda sun yi taho-mu-gama da masu zanga-zanga, ranar Litinin a Nairobi babban birnin Kenya, yayin da shugabannin addini da na diflomasiyya suka shawarci shugaban ƙasar da jagororin adawa su zauna kan teburin sulhu.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lokacin salla ne ya yi a masallacin Imam al-Shai'i da ke birnin al-ƙahira ranar Laraba.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani abu da aka saba gani a Sudan lokacin Ramadan, shi ne tsayar da matafiya da maraice don su tsaya su yi buɗe-baki da 'yan gari a gefen titi, abin da wannan mutumin yake yi ke nan a birnin Khartoum ranar Asabar.
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wani mahayin doki a bakin tekun Tangier da ke ƙasar Moroko a ranar Asabar.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Talata mawaƙiyar nan Fatoumata Diawara ta ɗauki hoto a Paris babban birnin Faransa.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mawaƙiyar Saharawi Aziza Brahim na waƙa ranar Juma'a a Sifaniya.