Chelsea ta ɗauki ɗan bayan Boca Juniors Anselmino £15m

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta kammala ɗaukar ɗan wasan bayan Boca Juniors Aaron Anselmino kan kuɗi fan miliyan 15.5.
Dan shekara 19 ya sanya hannu kan kwantaragi shekara bakwai a Stamford Bridge amma zai ci gaba da zama a Argentina a matsayin aro har zuwa kakar 2024-25, wannan na cikin yarjejeniyar cinikin.
A watan Yunin 2023 ne ya fara bugawa Boca Juniors wasa, kuma ya zuwa yanzu ya buga mata wasanni 10 baki ɗaya.
Anselmino ya tsawaita kwantaraginsa a watan Janairun 2024 inda zai ci gaba da zama a ƙungiyar har zuwa 2028.
Ya zuwa yanzu, Chelsea ta kashe fan miliyan 115 kan Kiernan Dewsbury-Hall da Renato Veiga da kuma Omari Kellyman, haɗi da mai tsaron raga Filip Jorgensen,da Tosin Adarabioyo da kuma Caleb Wiley, sai kuma ɗan wasan gefe Estevao Willian da ɗan wasan gaba Marc Guiu.
Ta kuma samu kuɗin da suka kai fan miliyan 90 kan 'yan wasan da ta sayar da suka haɗa da Ian Maatsen da Lewis Hall da kuma Omari Hutchinson, yayin da ake tsammanin za a samu fan miliyan 33 kan Conor Gallagher da ke shirin komawa Atletico Madrid.
Blues ta buɗe idonta wajen neman ɗan wasan gaba inda take son ɗauko Samu Omorodion daga Atletico Madrid.
Chelsea za ta fara wasanta na farko na kakar 2024-25 da mai riƙe da kofin Manchester City a ranar 18 ga watan Agusta.











