Vinicius ya buga wasa na 200 a La Liga a Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Valencia a La Liga a Santiago Bernabeu ranar Asabar, wasa na 200 da Vinicius ya yi kenan a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Ranar Asabar Valencia ta je ta doke Real Madrid da ci 2-1 a karawar mako na 30 a La Liga, yanzu saura wasa takwas-takwas a kammala wasannin bana.
Ɗan wasan Brazil, wanda ya ɓarar da fenariti ranar ta Asabar, shi ne ya ci wa Real ƙwallo a wasan, kuma na 11 a gasar bana na 20 da ya zura a raga a dukkan karawa a Real.
Vinicius yana kaka ta bakwai a Real Madrid, wanda aka yi nasara 131 da shi a Real Madrid da zura ƙwallo 61 a raga a La Liga da lashe kofin karo uku a 2019-20 da 2021-22 da kuma 2023-24.
Ƙungiyar da ya ci ƙwallaye da yawa a tarihi a La Liga sun haɗa da Villareal da Real Betis da kowacce ya zura mata 12 a raga.
Sai Valencia da ya ci tara da kuma Osasuna da ya zurawa takwas a raga daga jerin waɗanda ya ci ƙwallaye da yawa a La Liga tun komawarsa Real da taka leda.
Kakar da Vinicius ya buga wasa da yawa ita ce ta 2020/21 da kuma 2021/22 da kowacce ya yi wa Real fafatawa 35.
Yanzu dai Real Madrid, mai rike da La Liga tana ta biyun teburi da tazarar maki huɗu tsakani da Barlona ta ɗaya, wadda ta tashi 1-1 da Real Betis ranar Asabar.
Ranar Talata Real Madrid za ta buga wasan farko a kwata fainal da Arsenal a Emirates a Champions League.











