Copa del Rey: Batu biyar kan wasan Barca da Atletico

Barca Atletico

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Barcelona za ta fafata da Atletico Madrid a wasan farko zagayen daf da karshe a Copa del Rey ranar Talata a Estadi Olimpic Lluis Companys.

Wannan shi ne karo na biyu da za su kece raini a tsakaninsu a bana, bayan karawa a La Liga ranar 21 ga watan Disamba, inda Atletico ta ci 2-1.

Karon farko da Atletico ta yi nasara a gidan Barcelona tun bayan shekara 18, tun daga nan ba a kara cin Barcelona ba a dukkan wasa 13 da yin canjaras biyu daga ciki.

Kenan Barcelona ba ta yi rashin nasara ba a 2025 a dukkan fafatawa kawo yanzu.

Ge jerin batu biyar kan wasan Barcelona da Atletico Madrid:

Fitila ta haska Barcelona a karawar

A fafatawar nan ana ganin Barcelo ce za ta yi nasara, saboda wasa uku da suka yi a baya gida da waje, ƙungiyar Camp Nou ce ta kai zagayen gaba.

Barcelona na fatan a karon farko ta kai wa zagayen gaba karo na huɗu a jere a kan Atletico Madrid.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kowacce tana da mai cin ƙwallaye da yawa a Copa del Rey

Ɗan wasan Barcelona, Ferran Tores da na Atletico Madrid, Julian Alvarez kowanne ya zura ƙwallo huɗu a raga a Copa del Rey, haka kuma Sorloth na Atletico ya ci uku a wasannin.

Ƙungiyoyin sun ci ƙwallaye da yawa a Copa del Rey

Cikin wasannin da Barcelona ta yi a gasar ta bana ta ci ƙwallo 14 an zura mata ɗaya a raga.

Ita kuwa Atletico ƙwallo 15 ta ci kuma itama ɗaya ne ya shiga ragarta.

Sun daɗe suna haɗuwa a tsakaninsu

Wannan shi ne karon farko da Barca da Atletico za su fuskanci juna a gasar tun bayan 2016-17, Ter Stegen na Barcelona shi kaɗai ne ya rage tun daga lokacin, amma yana jinya.

Ita kuwa Atletico tana da ƴan ƙwallo uku da suka yi wasan na 2016/17 da suka haɗa da Koke da Correa da kuma Griezmann.

Wanann shi ne wasa na 19 da Simeone zai kai ziyara Barcelona

Diego Simeone, wanda ya fara horar da Atletico cvikin Disambar 2011, ya kai ziyara gidan Barcelona karo 18 a baya, sau ɗaya ya yi nasara shi ne 2-1 a Disambar 2024 da suka kara a Estadi Olímpic Lluis Companys.