Gasar tseren mata da tsaftar Muhalli cikin hotunan Afrika

.

Asalin hoton, RODGER BOSCH/AFP

Bayanan hoto, Masu goyon bayan 'Kungiyar Springboks a Afirka ta Kudu ranar Juma'a.
.

Asalin hoton, PETER FOLEY/EPA

Bayanan hoto, Kwana daya bayan zanga-zangar yar wasan tsere daga Kenya tare da 'yarta bayan ta yi nasara a tseren mata da aka gudanar a birnin York City.
.

Asalin hoton, JAMES WAKIBIA/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, James Githae shugaban ƙungiyar masu kwashe shara ta Nakuru, wadda za ta yi aikin tsaftar muhalli a Kenya ranar Laraba.
.

Asalin hoton, SIA KAMBOU/AFP

Bayanan hoto, A ranar Asabar, Sarki Amon Paul Désiré Tanow ya halarci bukin al'adun gargajiya a Kasar Ivory Coast
.

Asalin hoton, PEDRO VILELA/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Marc Diakiese 'dan damben Jamhuriyar Dimukuradiyyr Kwango ya fuskanci abokin karawarsa a gasar UFC da aka gudanar a Brazil ranar Juma'a.
.

Asalin hoton, RIJASOLO/AFP

Bayanan hoto, A ranar ne kuma Jami'an Tsaro suka harb wa masu zanga-zanga hayaki mai sa hawaye a babban birnin Madagascar.
.

Asalin hoton, RIJASOLO/AFP

Bayanan hoto, Yan adawa da masu goyon bayansu sun samu raunuka yayin zanga-zangar, makonni biyu kafin zaben shugaban kasa.
.

Asalin hoton, MICHELE SPATARI/AFP

Bayanan hoto, Mabiya Addinin Kirista a Habasha na tattaki a birnin Addis Ababa.
.

Asalin hoton, LEGNAN KOULA/EPA

Bayanan hoto, Jama'a sun yi dandazo don bukin al'adun gargajiya na Abissa a Kasar Ivory Coast ranar Asabar.
.

Asalin hoton, KHALED ELFIQI/EPA

Bayanan hoto, Ranar Talata lokacin da ma'aikata suke zuba gishiri cikin buhuna a tafkin Bardawel dake Kasar Masar
.

Asalin hoton, JEROME FAVRE/EPA

Bayanan hoto, A ranar ne sojoji suka gudanar da fareti don girmama ranar sojoji a Dakar baban birnin kasar Senegal.
.

Asalin hoton, ERNEST ANKOMAH/GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Magoya bayan jam'iyya mai mulki a Ghana NPP na wakoki kafin sanar da Mahamudu Bawumia a matsayin dan takarar shugaban kasa.
.

Asalin hoton, FEISAL OMAR/REUTERS

Bayanan hoto, Ambaliyar ruwa a Mogadishu babban birnin Kasar Somalia ta haifar da cunkoson ababen hawa.