Za a sake maimaita damben Rabe da Autan na Aisha a Maraba

An shirya sake damben gargajiya na gasa tsakanin Rabe Shagon Ebola da Autan na Aisha ranar Lahadi.
Za a yi karawar da za ta ja 'yan kallo a damben safe a Marabar N'yanya karamar huhumar Karo jihar Nasarawa, Najeriya.
A ranar 1 ga watan Oktoba ne aka hada damben gasa tsakanin dan wasan Kudu da na Guramada da suka yi turmi uku.
Koda yake Autan na Aisha ne ya buge Rabe Shagon Ebola a fafatawar da suka yi, waɗanda tun farko suka sha kiɗan makaɗin 'yan dambe Labaran dan Gwamba.
Lokacin da suka taka dambe a turmin farko Rabe ne ya dunga kora Autan na Aisha, wanda ya dunga fita daga filin dambe.
A turmi na biyu da na uku ma dai abin bai canja ba, inda Autan na Aisha baya tsayawa - daga nan ne Idris Bambarewa Sarkin yakin masu gidajen dambe ya umarci Rabe da ya bi Autan na Aisha wajen da'ira ya buge shi kuma kisa ne.

Koda yake Rabe ya gurɗa kafada ana tsaka da dambe a turmi na biyu, an kuma buƙaci a raba wasan, amma ya ce zai ci gaba da gumurzun.
'Yan wasan biyu sun sami kudi da yawa daga magoya baya, inda aka dinga yi musu likin kudi daga kowacce kusurwar filin.
Bayan da aka duba hannun Rabe ne bayan turmi na biyu, sai suka fada na uku, inda alkalin wasa Anas Dan Dume na busa wasan sai Rabe ya bi Autan na Aisha da duka.
Shi kuwa Autan na Aisha sai ya je bakin buhu, inda ya yi nasarar buge Rabe Shagon Ebola - Magoya bayan Rabe sun yi kokarin cewar ba kisa bane, amma daga baya an zagaya da Autan Na Aisha.
Wasu wasannin da za a buga a ranar Lahadi a damben Safen har da na Dan Aliyu da Shagon Yahayan Tarasa da na Garkuwan Cindo da Dogon Messi.











