Duran na daf da komawa Al-Nassr ta Saudi Arabia daga Aston Villa

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Aston Villa, Jhon Duran na daf da komawa buga babbar gasar tamaula ta Saudi Arabi a Al-Nassr, in ji wata majiya da ta sanar da BBC.
An cimma yarjejeniya kan kuɗin cinikin ɗan ƙwallon - wanda ya yi zaman benci a wasan da Villa ta doke Celtic ranar Laraba a Champions League - an auna koshin lafiyarsa ranar Alhamis.
An ce farashin ɗan wasan mai shekara 21 ɗan kasar Colombia ya kai £65m, amma BBC ba ta fayyace hakan ba.
Wata majiya daga wani babban jami'in gasar tamaula ta Saudi Arabia ta ce Duran zai koma Saudi Arabia ranar Asabar, idan an kammala koshin lafiyarsa cikin nasara.
Haka kuma an sanar da BBC cewar Duran ya yi ban kwana da abokansa da ma'aikatan Villa Park ranar Laraba, bayan da ciniki ya yi nisa tsakanin ƙungiyoyin biyu.
Duran ya koma Villa daga Chicago Fire kan £18m a Janairun 2023, amma yanzu zai bar Villa Park kan £64.4m har da karin tsarabe-tsarabe.
Al-Nassr tana mataki na huɗu a kan teburin babbar gasar tamaula ta Saudi Arabia ta bana.







