Waiwaye: Rasuwar Saratu Daso da bikin ƙaramar Sallah
Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.
Rasuwar fitacciyar 'yar Kannywood, Saratu Daso

Asalin hoton, SARATU FACEBOOK
A daren ranar Talata ne Allah ya yi wa fitacciyar 'yar Kannywood, Saratu Gidado da aka fi sani da Daso rasuwa.
Alhassan Kwalli wanda shi ne shugaban jarumai na Kannywood ya shaida wa BBC cewa marigayiyar ta yi rasuwar fuju'a ne bayan da ta shiga ɗaki ba ta fito ba.
"Tana zaune da iyalanta sai ta faɗa wa mutane cewa kowa ya je ya kwanta domin a ci gaba da ibada domin neman yardar Allah. To amma da safe ba a ga fitowarta ba har zuwa karfe ɗaya, to shi ne 'yan uwanta suka yi ta kwankwasa kofar har ta kai ga an ɓalle kofar, inda kuma aka gan ta rai ya yi halinsa." In ji Alhassan Kwalli.
Kafin dai rasuwarta, jarumar ta sha tattaunawa da BBC, inda a ciki take bujuro da bayanai daban-daban da masu kaunarta ke son ji dangane da ita kuma za mu yi tsakure.
Yadda Shugaba Tinubu ya yi sallah Eid a Dodan Barracks
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya yi sallah a filin Idi na Dodan Barracks da ke jihar Legas tare da mataimakin gwamnan Legas, Obafemi Hamzat.

Asalin hoton, Presidency

Asalin hoton, Presidency

Asalin hoton, Presidency
Yadda mai martaba sarkin Kano ya yi hawan sallah bayan Idi



Gwamnati ta ƙaddamar da shirin rabon hatsi tan 42,000 a Sokoto

Asalin hoton, @HMMohammedIdris/X
Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin rarraba tan dubu 42 na hatsi ga mabuƙata a jihar Sokoto.
Shirin wani ɓangare ne na umarnin shugaba Bola Tinubu na tallafa wa marasa galihu da abinci a halin matsin rayuwa da ake fuskanta a Najeriya.
Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan ranar Lahadi a shafinsa na X inda ya ce "na bi sahun gwamnan Sokoto, Ahmed Aliyu da abokan aikina, ministan noma da samar da abinci da ƙaramin minista Sabi Aliyu wajen ƙaddamar da rabon."

Asalin hoton, @HMMohammedIdris/X
Hukumar agaji ta ƙasar, Nema za ta sa ido kan rabon tare da taimakon hukumomin tsaro domin tabbatar da gaskiya.
A cewar saƙon na ministan, kowace jiha a ƙasar za ta ci gajiyar shirin kuma "za mu tabbatar mun bayar da ƙarin bayani kan shirin."
Tun farkon watan Maris ne shugaba Bola Tinubu ya bayar da amincewar a fara raba hatsin a faɗin jihohi 36 na ƙasar.
Majalisar Edo ta tsige mataimakin gwamnan jihar

Asalin hoton, @HonPhilipShaibu/X
A ranar Litinin ne Majalisar dokokin jihar Edo ta tsige mataimakin gwamnan jihar Philip Shaibu, bayan wani zama a Benin, babban birnin Edo.
Tsige Shaibu ya biyo amincewa da wani rahoton kwamitin mutum bakwai da alƙalin alƙalan jihar Daniel Okungbowa ya kafa domin yin bincike kan zarge-zargen aikata ba daidai ba da ake yi wa mataimakin gwamnan.
Ƴan majalisa 21 cikin 24 ne suka sa hannu kan takardar ƙorafin. Sun zargi Shaibu da yin ƙarya da kuma bayyana sirrikan gwamnatin jihar.
Tsige Shaibu na da nasaba da takun saƙar siyasa da ke tsakaninsa da ubangidansa Godwin Obaseki.
Sai dai a wani jawabi da Shuaibu ya yi ya ce majalisar dokokin jihar ba ta bi ƙa'ida ba wajen tsige shi.
A jawabin da ya yi ta bidiyon da ya wallafa a shafinsa na X, Philip Shaibu ya yi tur da matakin inda ya ce barazana ne ga dimokradiyya.
CBN ya kori ma'aikata fiye da 100 bisa zargin almundahana

Asalin hoton, CBN
Babban bankin Najeriya CBN ya kori ma'aikata sama da 117 a cikin abin da bai gaza kwana 20 ba.
BBC ta gano lamarin ya fi shafar manyan ma'aikata masu matsayin darekta da mataimakansa a sassan bankin guda uku da suka hada da sashen da ke kula da tallafi da mai kula da kwantaragi da kuma mai kula da lafiya da magunguna.
Yanzu mafi yawan ma'aikatan bankin cikinsu ya ɗuri ruwa saboda rashin sanin mai gobe za ta haifar.
Wata majiya daga bankin dai ta shaida wa BBC cewa korar yanzu aka fara domin "ba ma a zo sashen da ke kula da hada-hadar kudaden musaya ba."
Babu dai wanda ya yarda BBC ta naɗi muryarsa kan lamari, wasu na cewa ko hukumomin bankin ba za su iya cewa komai ba saboda rashin sanin inda aka dosa.
CBN na ci gaba da bincike kan badaƙalar da aka tafka tun daga wasu shekaru da suka wuce baya.
An tura Bobrisky gidan maza har na tsawon wata shida

Asalin hoton, Getty Images
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta ɗaure Idris Olanrewaju Okuneye wanda aka fi sani da Bobrisky a gidan yari ba tare da wani zaɓin biyan tara ba.
Mai shari’a Abimbola Awogboro ya yanke wa Bobrisky hukuncin watanni shida, wanda ke tsare tun bayan kama shi a makon jiya.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC dai ta gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhume-tuhume shida.
An yi watsi da tuhume-tuhume biyu, yayin da ya amsa laifin cin zarafin Naira, amma ya nemi a yi masa afuwa a matsayinsa na wanda ya fara aikata laifi.











