Amurka da ƙawayenta sun buƙaci a dakatar da buɗe wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah

Hari a rikicin Isra'ila da Lebanon

Asalin hoton, Reuters

Lokacin karatu: Minti 3

Kasashen da ke kawance da juna da suka hada da Amurka da Birtaniya da Faransa da kuma Tarayyar Turai sun yi kira da a dakatar da bude wuta ta wucin-gadi a Lebanon bayan da rikici ya rincabe tsakanin Isra’ila da kungiyar Hezbollah.

Kawayen sun gabatar da shawarar ne yayin da Babban Sakataren Majalisar dinkin Duniya ke gargadin cewa rikicin na neman zunguro sama da kara.

Kawayen masu karfin fadi a ji, da suka kunshi mambobi 12 sun bayar da shawarar da dakatar da bude wutar ta nan take ta tsawon kwana 21 domin samar da damar diflomasiyya don a samu a sasanta rikicin da kuma dakatar da bude wuta a yakin Gaza.

A wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar sun ce dauki-ba-dadin da ake yi abu ne da ba za a lamunta da shi ba a cewarsu kuma abu ne da ke iya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin rikici, wanda hakan ba abin da al’ummar Isra’ila ko Lebanon ba ne za su so.

Kiran ya biyo bayan babban hafsan sojin Isra’ila ya gaya wa dakarunsa a ranar Laraba cewa miyagun hare-haren sama da suke kaiwa a kan yankunan Hezbollah a Lebanon ka iya bude musu hanyar shiga yankin, wanda ya kira na abokan gabarsu.

Kalaman na Laftana Janar Halevi sun nuna karara cewa lalle ba makawa Isra’ila na shirin tura dakaru ta kasa cikin Lebanon.

Amurka da Australia da Kanada da Saudi Arabia da Hadaddiyar Daular Larabawa da Birtaniya da Qatar da Tarayyar Turai da Faransa da Jamus da Italiya da Japan ne suka sanya hannu a sanarwar hadin gwiwar.

Sanarwar ta kuma biyo bayan taron shugabannin duniya a babban taron majalisar dinkin duniya a New York.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Haka kuma a wata sanarwar ta hadin gwiwa ta daban da shugaba Biden na Amurka da takwaransa Emmanuel Macron suka fitar sun ce lokaci ya yi da za a sasanta domin bai wa fararen hula damar komawa gidajensu.

Suka ce rikcin da ake yi yanzu ka iya tazzara a yankin tare da cutar da fararen hula.

A wani dan takaitaccen jawabi da ya yi a fadarsa ta White House, a ranar Laraba Shugaba Biden ya ce, akwai gagarumin goyon bayan daga Tarayyar turai da kuma kasashen Larabawa – yana mai cewa abu ne mai muhimmanci a ga rikicin bai fadada ba.

Sai dai kuma wani babban jami’in gwamnatin Amurkar ya sheda wa BBC cewa, Isra’ila da Lebanon dukkaninsu ba wadda ta amince da shawarar - kodayake Amurkar na tuntubar dukkanin bangarorin biyu – kuma ana sa ran jin ta bangarensu cikin ‘yan sa’o’i..

Jami’in Amurkar ya ce tsagaita wutar ta tsawon kwana 21, za ta bayar da damar karin tattaunawa ta yadda za a cimma yarjejeniya mai sarkakiya.

Ya ce Amurka na tattaunawa ne da gwamnatin Lebanon ba kungiyar Hezbolah ba, yana mai karin bayani da cewa daga nan ne ita kuma gwamnatin Lebanon alabasshi sai ta yi magana da Hezbollah.

Tun da farko Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci da a dakatar da bude wuta nan take, yana mai cewa al’amura sun rincabe.

Firaministan Lebanon Najib Mikati ya ce kasarsa na fuskantar tsabagen keta haddin ‘yancinta da kuma hakkin dan’Adam daga abubuwan da abokan gabarsu, Isra’ila ke yi.

Shi ma da yake magana tun da farko jakadan Isra’ila a majalisar dinkin duniya Danny Danon ya ce abin a yaba ne yadda ake kokarin diflomasiyya na ganin rikicin bai fadada ba, amma kuma ya ce za su yi amfani da duk wata dama da suke da ita bisa tanadin dokokin duniya don cimma manufarsu.

Ya ce Isra’ila ba ta nufin cikakken yaki kuma ta nuna aniyarta ta samun zaman lafiya.

Mr Danon ya ce a yau Alhamis Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu zai sauka a New York, inda zai tattauna da Amurka, a ranar sannan kuma gobe ya yi jawabi a Babban taron majalisar.