Barcelona ta koma ta biyu a teburin La Liga bayan cin Sociedad

Barcelona

Asalin hoton, Getty Images

Barcelona ta koma ta biyu a teburin La Liga, bayan da ta doke Real Sociedad a wasan mako na 35 da suka fafata ranar Litinin a Estadi Olímpic Lluís Companys.

Barcelona ta fara cin kwallo ta hannun Lamine Yamal a minti na 12 da fara wasan, kuma haka suka je hutu, kungiyar da Xavi ke jan ragama na cin 1-0.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Barcelona ta kara na biyu a daf da za a tashi daga wasan ta hannun Raphinha a gudun daga kai sai mai tsaron raga.

Da wannan sakamakon Barcelona ta koma ta biyun teburi da maki 76, saura wasa uku a gabanta, yayin da Girona ta yi kasa zuwa ta uku da maki 75.

Ita kuwa Sociedad tana ta bakwai a teburi da maki 54, bayan da saura wasa uku a kammala kakar bana ta La Liga.

Wannan shi ne karo na biyu da suka kara a tsakaninsu a bana, inda Barcelona ta je ta ci 1-0 ranar 4 ga watan Nuwambar 2023, kuma Ronald Araujo ne ya ci kwallon.

Barcelona, wadda za ta buga Champions League a badi na fatan samun damar buga Spanish Super Cup, bayan da ta kasa kare kofin La Liga na bara da ta dauka.

Ana buga Spanish Super Cup ne tsakanin wadanda suka buga wasan karshe a Copa del Rey da wadda ta lashe La Liga da ta biyun teburin kakar.

Ranar Talata Girona za ta karbi bakuncin Villareal a wasan mako na 37 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, da zarar ta yi nasara za ta koma ta biyun teburi.

A karshen mako Real Madrid ta yi bikin lashe kofin La Liga na bana na 36 jimilla, ita ce kan gaba a yawan daukar kofin.

Real Madrid za ta buga wasan karshe da Borussia Dortmund a Champions League ranar 1 ga watan Yuni a Wembley.

Real tana da kofin zakarun Turai 14, ita kuwa Dortmund tana da daya, wadda karo na uku da za ta fafata a wasan karshe a gasar.

Ƴan wasan da suka fuskanci Sociedad a ranar ta Litinin.

Ƴan wasan Barcelona:

Ter Stegen, ⁠João Cancelo, R. Araujo, I. Martinez, Ferran, Pedri, Lewandowski, Raphinha, Iñaki Peña, João Félix da kuma Christensen.

Sauran sun hada da Fermín, Marcos A., Romeu, Vitor Roque, S. Roberto, Gündoğan, Kounde, Lamine Yamal, Kochen, Cubarsí da kuma H. Fort.