Bahagon Ƴansanda ya buge Shagon Ƴar biyat a damben Maraba

Damben Gargajiya

Ƙungiyar damben gargajiya ta ƙasa reshen jihar Nasarawa a Najeriya ta gabatar da wasanni da yawa, bayan da ta gabatar da ajon Bahagon Ali Kawoji ranar Lahadi da safe.

Hakan ne ya sa ta tsara damben gasa tsakanin Bahagon Shagon Ƴansanda da Autan Ƴar biyat na naira 100,000.

Wasa ne tsakanin ɗan wasan Arewa da na Guramada, waɗanda Labaran ɗan Gwamba ya wake kafin daga baya su shiga fili, bayan da masoya suka yi musu liki kuɗin.

Anas dan Dume shi ne alƙalin wasa, wanda ya kama hanunsu ya ɗaga da cewar sune a kan layi.

Ana take dambe a turmin farko Bahagon Ƴansanda daga Arewa ya buge Autan Ƴar biyat Guramada.

Haka kuma an rufe fili da damben Bahagon Autan Mamman da Autan na Aisha, shima na naira 100,000 karo na biyu da suka fuskanci juna a Marabar ƳNanya.

Turmi biyu suka taka ba kisa aka raba su, bayan da Bahagon Autan Mamman ya ji rauni a hannu, dalilin hakan aka hakura da damben.

Wasannin da aka yi kisa:

Damben Gargajiya
  • Autan na Malika ya buge Shagon Shagon Inda
  • Shagon Yalo ya yi nasara a kan Shagon Shagon Inda
  • Aljanin Nokiya ya doke Shagon Maru
  • Aljanin Nokia ya buge Autan Maru
  • Bahagon Yahaya ya yi nasara a kan Shagon Aliyu

Wasannin da aka yi canjaras:

  • Shagon Shamsu da Jan Idon Guramada
  • Autan Isa da Shagon Autan dan Bunza
  • Autan Fafa da Dan Sama'ila Shagon Alabo
  • Bahagon Ali Yaro da Autan Sanin gidan ɗan Kande
  • Bahagon Ali Kansila da Dogon Inda
  • Ilele Garkuwan mai caji da Bahagon Alin Tarara