'Zuwan Mbappe Real ba zai hana Bellingham rawar hantsi ba'

Asalin hoton, Getty Images
Matsayin Jude Bellingham a Real Madrid ba zai canza ba a bana, bayan ɗaukar Kylian Mbappe, in ji Carlo Ancelotti.
Bellingham ɗan wasan Ingila, mai shekara 21, ya taka rawar gani a Sifaniya a kakarsa ta farko, wanda ya zura kwallo 23 a wasa 42.
Yana cikin ƴan wasan da suka taka rawar gani a Real Madrid, wadda ta lashe La Liga da Champions League a kakar da ta wuce.
Mbappe, kyaftin ɗin tawagar Faransa, mai shekara 25, ya koma Real Madrid a bana daga Paris St Germain, bayan da ƙwantiraginsa ya kare a watan Yuni.
Ancelotti ya yi watsi da batun cewa Bellingham ba zai ke buga gurbin da ya saba a Real Madrid ba, domin bai wa Mbappe dama, ya kara da cewar: "Babu wani abu da zai canza a gare shi.
"Kakar farko, ya bai wa mutane mamaki, saboda yadda ya nuna ƙwarewa, yanzu kuma ya kara samun gogewa. Kenan wannan kakar haka zai ci gaba da taka rawar gani.
''Zai ci gaba da zama fitatcen ɗan wasan Real, wanda zai ci gaba da taka rawar da ƙungiyar za ta ci gaba da samun nasarori.''
Ancelotti ya goyi da bayan Bellingham, wanda aka dunga sukar ƙwazonsa a Euro 2024, duk da cewar Ingila ta kai wasan karshe a gasar.
"Wannan ra'ayi na ne, amma Bellingham ya taka rawar gani sosai a gasar cin kofin zakarun Turai ta Euro 2024," in ji Ancelotti.
"Ingila ta taka rawar gani sosai, wadda ta kai wasan karshe, kuma ƙaɗan ya rage ta lashe kofin.''
Ancelotti ya kuma bai wa masu Chelsea shawara da su kara hakuri da duk kocin da suka ɗauka, bayan da suka kori Thomas Tuchel da Graham Potter da Mauricio Pochettino.
Tsohon kocin Chelsea zai fuskanci Enzo Maresca a wasan sada zumunta tsakanin Real Madrid da Chelsea a Amurka ranar Talata a Charlotte.











