Manyan ƙungiyoyin Premier League na harin Diomande, Axel Disasi zai koma Fransa

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool da Manchester City na son ɗaukar ɗan wasan RB Leipzig Yan Diomande. (Caughtoffside)
Axel Disasi na Chelsea zai koma Lyon, sakamakon yadda ƙungiyar ke son ɗaukar ɗan wasan a matsayin aro. (L'Equipe - in French)
Aston Villa za ta ɗauki ɗan wasan Starsbourg mai shekaru 23 Joaquin Panichelli, yayin da Chelsea da West Harm ke sa ido akansa. (Teamtalk)
Leeds ta fara tataunawa da Como kan siyen ɗan wasan ta mai shekaru 23, Martin Baturina, sai dai ƙungiyar da ke Italiya ta ƙi amincewa da tayin. (Fabrizio Romano via Yorkshire Post)
West Ham da Crystal Palace na son ɗaukar ɗan wasa Samson Baidoo, mai shekaru 21, don ƙara inganta tsaron bayan ƙungiyar. (Teamtalk)
Newcastle zata siyi ɗan wasa Alex Toth, mai shekaru 20, kan Fam miliyan 15, sai dai Ferencvaros da ya ke taka wa leda har zuwa 2027, ce za ta fi yanke farashin da za ta siyar da shi. (Chronicle)
Newcastle na son ɗaukar ƴan wasa daga Brazil, a yuƙurinta na zaɓo matasan ƴan wasa daga Latin, a kakar siyen ƴan wasa mai zuwa. (ESPN)
Liverpool zata siyo ɗan wasan Galatasary Wilfried Singo mai shekaru 24 kan fam miliyan 38. (Fotomac and Foot-Sur7 via SportWitness)











