Da gaske Amurka na shirin faɗawa karayar tattalin arziki?

Wani burkila yana taimakawa wajen gina wani rukunin gidaje

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Natalie Sherman
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 3

Yayin yaƙin neman zaɓensa a shekarar da ta gabata, Donald Trump ya yi wa Amurkawa alƙawarin cewa zai haɓaka rayuwarsu ta tattalin arziki.

Yanzu wata biyu a mulkinsa, abubuwan ba haka suke ba.

Ya yi gargaɗin cewa abu ne mai wahala a sauko da farashin kayayyaki kuma ya kamata mutane su kasance cikin shirin "shiga 'yar wahala" kafin ya iya shawo kan lamarin.

A gefe guda kuma, masu sharhi na ganin alamun shiga matsala na ƙaruwa musamman duba da tsare-tsarensa.

Ko Trump na ƙoƙarin jefa tattalin arziki mafi girma a duniya cikin karaya?

Faɗuwar hannun jari mai ta'azzara yanayi

A Amurka, karayar tattalin arziki na nufin cikas mai tsawo kuma mai faɗi game da tattalin arziki kamar ƙaruwar rashin aikin yi da kuma raguwar kuɗaɗen da 'yan ƙasa ke samu.

Masu sharhi da yawa na ganin ana ƙara tunkarar irin wannnan yanayin a Amurka yanzu haka.

Wani rahoto na bankin JP Morgan ya ce akwai yiwuwar faɗawa cikin karayar tattalin arziki kashi 40 cikin 100, wadda ta ƙaru daga kashi 30 a farkon shekarar nan.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shi kuma Mark Zandi, babban jagoran nazarin tattalin arziki a cibiyar Moody's Analytics, ya ƙara yawan yiwuwar daga kashi 15 zuwa kashi 35 cikin 100.

Rashin tabbas a kasuwanni na da nasaba ne da fargabar ƙarin haraji kan kayayyakin da ake shiga da su ƙasar daga waje da Shugaba Trump ya yi tun bayan kama mulkinsa.

Ya ƙaƙaba wa ƙawayen Amurkar uku ƙarin haraji kan kayayyakinsu, sannan ya ci gaba da yi musu barazana a fili, abin da masana ke cewa zai jawo hauhawar farashi kuma ya rage yawan kayan da ake samarwa.

Trump da masu ba shi shawara sun yi ta gargaɗin jama'a da su shirya wa abin da ka iya faruwa, yayin da suke rage girman matsalar.

"Za a yi ta samun sauye-sauye," a cewarsa makon da ya gabata game da roƙon da 'yankasuwa ke yi na neman tabbaci.

Bankin Goldman Sachs ya ƙara yawan yiwuwar shiga matsalar daga kashi 15 zuwa 20 cikin 100, yana mai cewa sauyin da aka samu a tsare-tsaren tattalin arziki "a matsayin babban dalili".

"Idan fadar White House ta ci gaba da aiwatar da manufofinta, yiwuwar faɗawa karaya za ta ƙaru," a cewar babban mai nazari na bankin.

Haraji, rashin tabbas, da jan ƙafa

Babban abin da ya fi damun kamfunna shi ne haraji, wanda zai ƙara yawan kuɗin da suke biya. Yanzu kuma kamfunna na fama da ƙarancin riba, wanda ya sa suka rage yawan ma'aikatan da suke ɗauka da jarin da suke zubawa.

Masu zuba jari ma na fargabar rage ma'aikata da gwamnatin Trump ke shirin yi, da rage kuɗin da take kashewa.

Brian Gardner, shugaban tsare-tsare a bankin Stifel mai zuba hannun jari, ya ce 'yankasuwa sun zaci Trump na neman yin amfani da ƙarin harajin ne a matsayin makamin tattaunawa.

"Amma abin da shugaban da tawagarsa ke yi na nuna akwai babban al'amari. Sauya tsarin tattalin arzikin Amurka ne," a cewarsa. "Kuma wannan ne ke tunzira kasuwar tun daga 'yan makonnin da suka wuce."

Da ma can tattalin arzikin na Amurka na fama da matsala saboda dalilai kamar matakin babban banki na saka kuɗin ruwa mai yawa da zimmar kwantar da hankulan harkoki da kuma farashi.

Alƙaluma na baya-bayan nan sun nuna ƙaruwar rauni a tattalin arzikin.

Yawan sayar da ɗaiɗaikun kayayyaki ya ragu a watan Fabrairu, ƙwarin gwiwa ma ya ragu, kamfunna har da na jiragen sama duka suna barazanar janyewa.

Wasu na fargabar raguwar haɓakar kasuwar hannun jari za ta iya ƙara ta'azzara matsalar kashe kuɗi, musamman kan iyalan da samunsu yake da ɗan yawa.

Shugaban babban bankin Amurka, Jerome Powell, ya bayar da tabbaci a jawabinsa makon da ya gabata.

"Duk da matsalar rashin tabbas, tattalin arzikin Amurka na ci gaba da kasancewa cikin yanayi mai kyau," in ji shi.

Amma yanzu haka tattalin arzikin na Amurka na dogara ne da sauran na duniya, kamar yadda Kathleen Brooks, mai bincike a XTB, ta bayyana.

Kasuwar hannun jari

Rashin tabbas ɗin da ake fama da shi a kasuwa ba a kan Trump kawia ya ƙare ba.

Masu zuba jari ma tuni suka fara ɗari-ɗari da sauyin da za a iya samu bayan gagarumar ribar da aka samu sakamakon girmamar kasuwar ƙirƙirarriyar basira ta AI.

Misali, kamfanin ƙirƙira na Nvidia ya samu ƙarin riba a hannayen jarinsa daga dala 15 a farkon 2023 zuwa kusan 150 a Nuwamban shekarar da ta gabata.

Irin wannan tagomashin ya jawo muhawara game da basirar AI - inda ta sa masu zuba jari suka fara kamewa, wanda zai iya yin tasiri ga kasuwar.

Yadda tattalin arzikin Amurka yake a yanzu, da wuya kyakkyawan zaton da ake da shi a kan AI ya iya ceto shi.