Camfe-camfe bakwai a kan shayar da jarirai nonon uwa

Wata ma'aikaciyar lafiya na yi wa mace bayani kan amfanin shayar da nonon uwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bai kamata mace ta riƙa jin zafi lokacin shayarwa ba
    • Marubuci, Efrem Gebreab
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Taken ranar shayarwar ta duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi shine neman goyon baya da ƙwarin guiwa ga mata domin shayarwa a wajen aiki.

Majalisar Ɗinki Duniya ta ce akwai yiyuwar yaron da ba a shayar da shi ba ya rasu sau 14 fiye da wanda aka shayar da shi nono uwa zallah.

Majalisar Ɗinki Duniya ta kuma yi kira da a riƙa biyan mata ma'aikata albashin su a lokacin da suke hutun haihuwa, tare da bada hutun ɗan lokaci a yayin aiki, a kuma samar da ɗakin shayarwa a kowace ma'aikata domin ba da dama ga mata masu shayarwa su shayar da yaran su.

Akwai wasu canfe-canfe kan shayarwa da ke hana wasu mata shayarwar.

BBC ta tattaro bayanai daga ƙwararri biyu domin tantance gaskiyar wasu daga cikin canfe-canfen.

Catriona Waitt farfesa ce a ɓangaren haɗa magunguna da al'amurran da suka shafi lafiya ta duniya a jami'ar liverpool, kuma mai bincike ce a jami'ar Makerere ta Uganda, sai kuma Alastair Sutcliffe farfesa ne a ɓangaren cutukan da suka shafi yara a jami'ar Landan.

Camfi na biyu: Shayarwa akwai raɗaɗi kuma kan nono na kumbura

Farfesa Waitt: Amsar wannan ta na da sarƙaƙiya, saboda zafin da ake ji a farkon shayarwa akwai wanda bashi da aibu saboda hakan na faruwa ne kafin bakin nono ya buɗe, amman idan ya wuce ƙima ko ya ɗauki lokaci yana zafin to akwai damuwa, saboda bai kamata shayar da nono ya zama abu mai ciwo ba, sai dai idan bakin nonon na ɗauke da wasu ƙwayoyin cuta ko kuma ba a koyawa yaron yadda ya kamata ya riƙa jan nonon ba.

Idan har haihuwar farko ce, to akwai buƙatar a bi a hankali wajen koyawa Uwa yadda za ta shayar da nonon uwa ga jaririn ta, a kuma lura sosai domin tabbatar da cewa ciwon da take ji bai wuce ƙima ba, domin idan har ya wuce ƙima akwai buƙatar a je asibiti wajen mlamar jinya ko mai ƙarɓar haihuwa.

Camfi na biyu: Duk wadda ba ta fara shayarwa nan take ba, ba za ta iya ba daga bisani

Wata mata a lokacin bikin makon shayar da nonon uwa na duniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata mata a lokacin bikin makon shayar da nonon uwa na duniya

Farfesa Sutcliffe: Dukkan wani abin da zai ƙara bada ƙwarin gwiwa ga uwa wajen shayarwa to yana da amfani sosai a kowane mataki. Duk wani abin da ba na asali ba ga ɗabi'ar ɗan adam da aka ƙara to ba ya bisa ma'aunin kimiyya.

Amman akwai alfanu mai yawa game da ba jariri nono nan take da an haife shi.

Abinci mai inganci shine ya fi kowane abu mahimmanci. Yana taimakawa wajen rage yankewar jini da wasu matan idan sun haihu suke fuskanta.

Bayan ƴan wasu kwanaki da haihuwa, jiki yana fitar da wani sinadari mai amfani sosai ga lafiyar jariri, wanda jariri ke matuƙar buƙata farkon shayarwa.

...

Asalin hoton, Getty Images

Camfi na uku: Mai shayarwa ba za ta iya shan duk wani magani ba

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Farfesa Waitt: Wannan ita ce tambaya ta farko da kowace Uwa ke fara tambaya a faɗin duniya.

Shin duk maganin da na sha ba shida illa ga jaririna ? Gaskiyar magana shine kowane magani Uwa ta sha yana zuwa ga jaririnta amman sidarin ƙadan ke kai mashi. Idan lilita ya ce akwai buƙatar Uwa ta sha wani magani , za ta iya tambayarsa duk abin da ya shige mata duhu kan hakan, sai dai ba a buƙatar yawan shan magani ga mai shayarwa abin da jariri ke buƙata shine lafiyar mahifiyarsa.

Magungunan da ake yawan amfani da wajen magance cututtuka da cutar damuwa da kuma na kashe zafi ba su da illa ga jaririn da ake shayarwa.

A ɓangaren magungunan da ba a son amfani da su a lokacin shayarwa basu da yawa. Saboda yawancin su na manyan cututtuka ne, kamar irin ciwon daji.

Akwai sauran magungunan da dole a kula sosai kafin Uwa ta yi amfani da su saboda illolin da ke tattare da su da alfanun su. Duk macen da ke shayarwa idan aka rubuta mata magani ya kamata ta nemi ƙarin bayani daga wanda ya rubuta maganin kan rashin illarsa ga jaririnta.

Dole ne mai shayarwa ta guji zuwa wajen masu sayar da magani kai tsaye ba tare da rubutun likita ba, saboda akwai waɗanda ke ɗauke da sinadaren dake rage ruwan nono.

Uwa mai shayarwa ya kamata ta yi taka tsantsan wajen amfani da magungunan gargajiya saboda da yawan masu bada maganin ba ƙwararri bane.

Yawancin magunguna ba su da illa a lokacin shayarwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yawancin magunguna ba su da illa a lokacin shayarwa

Camfi na huɗu: Kafin fara shayarwa sai dai ki dinga cin abinci lami kuma ba ke babu yaji

Farfesa Waitt: Uwa za ta ci duk abin da take so a lokacin da take shayarwa.

Ko ya ke abincin da Uwa ke ci na taimakawa wajen samar da nonon Uwa.

Uwa ya kamata ta riƙa lura a lokacin da take shayarwa, kamar misali wata za ta ce idan sha lemu, jaririn ta yana shiga wani yanayi marar daɗi.

Saboda haka, dole kowace uwa ya kamata ta lura da kalar abincin da idan ta ci yake haifar da matsala ga jaririn ta.

A kimiyyan ce babu wani abinci da aka ware wanda aka hana uwa ci a lokacin da take shayarwa.

..

Asalin hoton, Getty Images

Camfi na biyar: Ba za ki iya amfani da madara ba idan za ki shayar

Farfesa Waitt: Wannan ba gaskiya ba ne. Abin da za a lura da shi a lokacin shayarwa shine, wadatar ruwan nono ga jaririn da ake shayarwa, ma'ana a lura da shin yaan ƙosar da jariri. Wani abin burgewa shine jikin mace yana samar da wadattacen ruwan nono ga jaririn ta. Indai jaririn zai ja nonon yadda ya kamata, to jikin ta zai samar da sidaran da ke kawo ruwan nono.

Misali idan uwa na shayar da jariri mai ƙaramin jiki ko babba ko kuma ƴan biyu, jikin ta zai samar da adadin ruwan nonon da suke buƙata.

Idan uwa ta fara da ba jaririnta madara, to akwai banbanci, saboda jikin ba zai riƙa samun alamun da yake buƙata ba wato tsotsar da jaririn zai riƙayi za ta yi ƙaranci, saboda haka ba za ta riƙa samar da wadataccen ruwan nono ba.

Idan ƙarancin ruwan nono ya sanya aka fara haɗawa jariri da madara to wannan ba mafita ba ce ta dindin, kawai dai Uwa za ta samu sauƙi na wani lokaci ƙalilan, amman hakan zai iya ƙara dagula matsalar.

A wani ɓangaren kuwa, idan har uwa ta gaji ne kuma akwai buƙatar ta huta, anan abokin zaman ta zai iya taimakawa da ba jaririn madara na wani lokaci musamman da dare domin ta huta, kuma hakan ba zai hana ta ci gaba da shayarwa da safe ba.

..

Asalin hoton, Getty Images

Camfi na shida: Maras lafiya ba za ta shayar ba

Farfesa Sutcliffe: Wannan camfi ne kawai. Hakan na faruwa ne kawai idan uwa na ɗauke da cuta HIV ko ciwon hanta, saboda a baya an samu masu waɗannan cututtukan da suka shafawa jaririn su ta hanyar shayar da su nono.

Saboda haka indai wata cuta ta daban ce take damun uwa, za ta iya ci gaba da shayar da jaririn ta saboda jikin ta zai riKa samar da wasu ƙwayoyin halitta da za su riƙa samar da kariya ga jaririnta.

..

Asalin hoton, Getty Images

Camfi na bakwai: Da wuya ki iya yaye jariri idan shayarwa ta wuce shekara ɗaya

Farfesa Waitt: Hukumar Lafiya ta duniya ta bada shawarar a shayar da jariri nonon uwa zalla na tsawon wata shida, sai kuma a fara bada abincin da ya dace ga jaririn da zai ƙara taimaka ma sa amman ba za a daina bashi nono ba har sai lokacin da uwa ta yi ra'ayin dainawa.

A ƙasashe masu arziƙi kamar misali Birtaniya, yawanci ana yaye jariri daga shekara ɗaya zuwa biyu. Sai dai wasu ƙasashe masu tasowa kamar Uganda ana yaye yaro daga shekara biyu zuwa uku.

Babbar matsalar da shayar da nonon uwa zalla ke fuskanta a duniya shine, ƙarancin hutun haihuwa da zai taimaka wajen shayar da nonon uwa zalla kamar yadda hukumar lafiya ke bada shawara.