Real Madrid ta ci Barcelona gida da waje a La Liga a El Clasico

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta doke Barcelona 3-2 a wasan mako na 32 a La Liga a Santiago Bernabeu da suka kara ranar Lahadi.
Barcelona ce ta fara cin kwallo a minti na shida ta hannun Andreas Christensen, yayin da Vinicius Junior ya farke a bugun fenariti.
Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Fermin Lopez ya ci wa Barcelona na biyu, amma Lucas Vazquez ya farke, sannan Jude Belligham ya kara na uku daf da za a tashi.
Da wannan sakamakon kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama tana ta daya a teburin La Liga da maki 81 da tazarar maki 11 tsakani da Barcelona ta biyu.
Girona ce ta uku mai maki 68 da kuma Atletico Madrid mai maki 61 a mataki na hudu a teburin babbar gasar tamaula ta Spaniya.
Wannan shi ne wasa na uku da suka kara a bana, inda Real Madrid ta je ta ci Barcelona a La Liga 2-1 ranar 28 ga watan Oktoban 2023.
Haka kuma Real Madrid ta doke Barcelona 4-1 a Spanish Super Cup ranar 14 ga watan Janairun 2014.
Wasannin da aka buga tsakanin Real Madrid da Barcelona 2023/2024:
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Spanish La Liga Lahadi 21 ga watan Afirilun 2024
- Real Madrid 3 - 2 Barcelona
Spanish Super Cup Lahadi 14 ga watan Janairun 2024
- Real Madrid 4 - 1 Barcelona
Spanish La Liga Asabar 28 ga watan Oktoban 2023
- Barcelona 1 - 2 Real Madrid
Barcelona ta ci karo da koma baya a Champions League a bana, bayan da Paris St Germain ta fitar da ita a zagayen daf da na kusa da na karshe.
PSG ta kai daf da karshe, bayan da aka doke ta 3-2 a Faransa, ita kuma ta ci 4-1 a Spaniya a wasa na biyu, kenan ta ci kwallo 6-5 gida da waje.
Barcelona ce ke rike da La Liga da ta dauka a bara, wadda rabon da ta lashe Champions League tun 2014/15 mai biyar jimilla.
Ita kuwa Real Madrid ta kai zagayen daf da karshe a gasar zakarun Turai, bayan da ta fitar da Manchester City a bugun fenariti, sakamakon da suka tashi 1-1 har da karin lokaci a Etihad.
Tun farko sun tashi 3-3 a Spaniya, kenan Real Madrid ta rama abinda City ta yi mata a bara da ta cire ta a Champions League.
Sakamakon asannin mako na 32 a La Liga ranar Lahadi 21 ga watan Afirilu:
Getafe 1-1 Real Sociedad
Almeria 1-2 Villarreal
Deportivo Alaves 2-0 Atletico Madrid
Real Madrid 2-2 Barcelona











