Me ya faru a turmutsutsun raba kayan Sallah da ya zo da ajalin mutum 78?

Asalin hoton, AFP
Aƙalla mutum 78 ne aka tabbatar sun mutu a turmutsutsun da ya auku cikin wata makaranta da ke Sanaa, babban birnin Yemen, lokacin wani rabon kayan Sallah, a cewar jami'ai.
Bidiyon talbijin sun nuna cincirindon mutanen da suka kasa motsawa, wasu da yawa kuma na cikin tashin hankali a unguwar Bab al-Yemen.
Ɗaruruwan mutane ne aka ba da rahoto sun cunkushe a makarantar da yammacin Laraba a ƙoƙarinsu na karɓar tallafin da ya kai kimanin naira dubu bakwai duk mutum ɗaya.
Tun a shekara ta 2015 ne 'yan tawayen ƙungiyar Houthi ta karɓe iko da birnin Sanaa.
Wani bidiyo da aka wallafa a shafin sada zumunta ya nuna mutae na ihun neman ɗauki, ga gomman gawawwaki kwance a ƙasa, ba sa motsi. Wasu mutane kuma suna ƙoƙarin ceto.
An kama 'yan kasuwa biyu na yankin waɗanda su ne suka shirya taron raba kayan tallafin kuma ana nan za a fara bincike, in ji ministan cikin gida.
Wani mai magana da yawun ma'aikatar ya ɗora alhakin turmutsutsun a kan "rabon tallafin kuɗi kara-zube" babu tsari tare da haɗa gwiwa da jami'an yankin.
Mutane da yawa kuma sun ji raunuka, wasu goma sha uku na cikin halin rai-kwakwai mutu-kwakwai, cewar wani jamin lafiya a Sanaa.
"Mata da ƙananan yara na cikin waɗanda suka mutu," kamar yadda wani jami'in tsaro na ƙungiyar Houthi ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Shi ma kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito wasu shadu guda biyu na cewa mayaƙan Houthi sun yi harbi cikin iska a ƙoƙarinsu na kwantar da ƙura, abin da ga alama ya taɓa wata wayar lantarki da ta yi tartsatsi. Lamarin da kuma ya janyo firgici har aka samu turmutsutsu, kamar yadda suka ƙara da cewa.
'Yan tawayen daga nan sai aka ce sun rufe makarantar kuma suka hana mutane ciki har da 'yan jarida isa.
An ba da rahoton cewa ƙungiyar Houth ta amince ta biya $2000 ga dukkan dangin da suka rasa wani nasu, yayin da za a biya waɗanda suka jikkata kimanin $400.
Wasu bayanai da alƙaluma game da Yemen
- Yemen ta ɗaiɗaice sanadin wani rikici da ya tsananta a shekara ta 2015, lokacin da mayaƙan Houthi suka ƙwace wani babban yanki na ƙasar kuma dakarun gamin gambiza ƙarƙashin jagorancin Saudiyya da tallafin gwamnatin Yemen
- Mutane fiye da 150,000 ne suka mutu a rikicin, wanda akasari ke gani a matsayin yaƙin 'yan baranda tsakanin Saudiyya da Iran
- Mutane fiye da miliyan 23 - kashi ɗaya cikin uku na al'ummar ƙasar - na cikin buƙatar wani nau'i na tallafi
- Gwamnatin Yemen da ƙasashen duniya ke martabawa a yanzu tana birnin Aden
Wannan lamari dai ya faru ne daidai lokacin da watan azumi mai alfarma na Ramadan ya zo ƙarshe.
A cikin makon jiya ne aka fara wani gagarumin musayar fursunoni tsakanin ɓangarorin da ke faɗa da juna a Yemen, ana kallon matakin a matsayin wani ɓangare na ƙarin ƙoƙari don kawo ƙarshen rikicin shekara takwas da ya ɗaiɗaita ƙasar.
Mohamed Ali al-Houthi, shugaban Kwamaitin Juyin-juya-halin Ƙoli na ƙungiyar Houthi ya ɗora alhakin turmutsutsun a kan halin tsananin buƙatun jin ƙai da ƙasar ke ciki.
"Muna ɗora alhakin abin da ya faru kan takalar faɗa daga ƙasashen waje da kuma tsagwaron matsin rayuwa da al'ummar Yemen ke ciki saboda aukawa ƙasar da yaƙi da kuma yi mata ƙofar rago," ya faɗa a shafinsa na Tuwita.











