Neymar ya tsallake rijiya da baya

Asalin hoton, Getty Images
Masu gabatar da kara a Spain sun janye tuhumar da suke yi wa Neymar rashawa da almundahana.
An zargi dan wasan gaban Paris St-Germain da Brazil da wasu mutane na daban kan komawarsa Barcelona daga Santos a 2013.
Tun da farko masu gabatar da karar sun nemi a aike da Neymar zuwa gidan yari na tsawon shekara biyu bayan tarar da za a ci dan wasan mai shekara 30 ta yuro miliyan 10.
Amma yanzu sun janye duka tuhume-tuhumen da ake yi wa dan wasan wanda suka gabatar tun da farko.
Sauran mutanen da ake zargi a wannan shari'a su ne iyayen Neymar da kuma kungiyoyin biyu da tsofaffin shugabannin Barcelona Josep Maria Bartomeu da Sandro Rosell, tsohon shugaban Santos Odilio Rodrigues.
Neymar wanda ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, yace babu ko hannunsa daya cikin wannan tattaunawar da aka yi.
A 2011 ne aka cimma yarjejeniya tsakanin Santos da Barcelona, wadda kuma aka cimma bayan shekaru biyu.
Kamfanin DIS, wanda ke da hakkin mallaka da yakai 40% na cinikin da dan wasan a wancan lokacin, ya ce ya yi asara a cinikin Neymar saboda rage masa kima da aka yi.
Neymar mai shekara 30 ya musanta zargin amma ya yi rashin nasara a karar da ya daukaka a Kotun Daukaka Kara a Sifaniya a 2017, wanda ya janyo masu gabatar da karar Sifaniyan suka ci gaba da aikinsu.











