Valencia ta doke Real a Bernabeu karon farko tun 2008

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Real Madrid ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Valencia a wasan mako na 30 a La Liga da suka fafata ranar Asabar a Santiago Bernabeu.

Valencia ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Diakhaby, daga baya Vinícius Júnior ya farke a zagaye na biyu.

Daf da za a tashi daga karawar Valencia ta ci na biyu a raga a cikin karin lokaci ta hannun Hugo Duro.

Real ta ɓarar da fenariti ta hannun Vinicius Jr, bayan da Cesar Tarrega na Valencia ya yi wa Kylian Mbappe keta.

Da wannan sakamakon Real ta ci gaba da zama ta biyu a teburin La Liga da tazarar maki uku tsakani da Barcelona, wadda za ta kara da Real Betis a ranar ta Asabar.

Real Madrid ta kasa cin fenariti biyar a kakar nan a dukkan karawa, wadda ta ci 11 daga 16 da ta samu.

Bayan da Thibaut Courtois ke jinya da Andriy Lunin, Real ta yi amfani da matashi mai shekara 19, Fran Gonzalez a matakin mai tsare raga.

Golan ya zama matashin da ya fara tsare ragar Real Madrid mai karancin shekara a La Liga tun bayan Iker Casillas, mai shekara 18 da kwana 115 a Satumbar 1999.

Wannan shi ne karon farko da Valencia ta yi nasara a Bernabeu tu bayan 2008.

Ƙungiyoyin biyu sun kara a bana ranar 3 ga watan Janairun 2025a gasar ta La Liga, inda Real ta je ta yi nasara da cin 2-1.

Kawo yanzu Real ta yi karawa 14 a gida, har da lashe wasa 11 daga ciki da rashin nasara a hannun Valencia.

Ranar Talata Real Madrid za ta kara da Arsenal a Champions League a Emirates zagayen farko a kwata fainal.

Ƴan wasan Real Madrid ta fuskanci Valencia:

Masu tsare raga: Lunin, Fran González da kuma Sergio Mestre.

Masu tsare baya: Alaba, Lucas V., Vallejo, Fran García, Rüdiger da kuma Asencio.

Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni da kuma Arda Güler.

Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick da kuma Brahim.